Ta dauki cikin danta za ta haifi jikarta
Ta matukar sadaukar da kanta a kanmu.
Wata mata da ke zaune a yankin Utan na Kasar Amurka, Nancy Hack na dauke da cikin danta kuma ana sa ran za ta haifi ’ya mace nan ba da jimawa ba.
Matar ta dauki kasadar taimakon danta Jeff mai shekaru 32 da matarsa Cambria mai shekaru 30, bayan matar da gaza sake daukar ciki sakamakon aiki da aka yi mata bayan haihuwar ’yan tagwaye da ta yi a baya.
- Za mu kwato yankunanmu 4 da Putin ya kwace —Zelensky
- Sojoji Sun Ceto ’Yar Makarantar Chibok Bayan Ta Haifi Tagwaye
Nancy mai shekaru 56 ta amince a dasa mata kwan haihuwar danta a mahaifarta domin haife abin da aka samu lami-lafiya ba tare da wata matsala ba.
Haka nan na ji ina so na taimaka musu. Lokacin da na sanar da dana fashewa da kuka ya yi, kuma ban fada wa mijina ba amma ya goyi bayan shawarar da na yanke, kamar yadda ta shaida wa tashar SWNS.
Maauratan sun shafe tsawon shekaru kafin samun karuwa, inda daga bisani suka samu haihuwar tagwaye; Vera da Ayva. Sannan suka sake haihuwar wasu tagwayen; Diseal da Luka.
Tun daga wannan lokacin mahaifiyar tagwayen ta shiga damuwa sakamakon aikin da aka yi mata a lokacin haihuwarsu, lamarin da ya sa ba za ta iya sake daukar wani kwan haihuwa ba a mahaifarta.
Jeff da Cambria na da sha’awar haihuwar yara da yawa, amma sun shiga damuwa kan abin da ka iya zuwa ya dawo bayan aikin da aka yi mata a 2021 kafin an da haihuwarta ta karshe.
Jeff ya ce, “Ina farin ciki sosai da na samu mahaifiya wadda ta iya sadaukar da kanta don farin cikin iyalaina.
“Da farko na yi tunanin dasa mata kwan haihuwar ba zai yiwu ba duba da yanayin shekarunta da kuma yadda ake aikin, amma abun mamaki komai ya tafi yadda ake so,” in ji shi.
Da farko Nancy ta yi niyyar taimakon danta, sai dai ta yi tunanin ba lallai aikin ya yi a jikinta ba.
“Na fada musu cewar ina son taimakon su, amma ban sani ba ko na yi tsufa. Sai dai likitoci sun bayyana cewar ina da lafiyar da zan iya daukar aikin, kuma ga shi komai na tafiya daidai.”
Iyalan da ke zaune a yankin Utah na kasar Amurka, sun shiryawa samun wata karuwar bayan yara hudu yanzu haka a raye
Nancy ta taba daukar ciki har sau biyar a rayuwarta kuma ba ta taba samun matsala ba wajen haihuwa.
Da farko, wasu daga cikin ’ya’yanta sun nuna damuwa, amma kuma daga bisani sun amince da ta taimaka wa dan uwansu.
A watan Fabrairun 2022 aka yi Nancy dashe kwayayen haihuwar Jeff da Cambria kuma komaí ya tafi daidai, inda take dauke da cikin jikarta.
“Na dan tsorata da farko saboda na shafe shekara 26 ba tare da na dauki ciki ba,” a cewar Nancy.
Jeff ya yi murna sosai kan yadda ya ga mahaifiyar na murmurewa bayan daukar cikin, inda ya ce tana cikin koshin lafiya kuma jikinta ya karbi juna biyun.
A watan Mayun 2022, iyalan sun yi murna matuka bayan an bayyana musu cewar mace Nancy za ta haifa.
Cambria ta ji dadin yadda uwar mijinta ta taimake su, “Ta matukar sadaukar da kanta a kanmu. Mun gode sosai.”
Iyalan na cikin farin ciki da jin dadi tun bayan da cikin ya fara girma, babu abin da kowa ke yi sai fatan a haife cikin lafiya.
Cambria da Jeff babu aikin da suke yi kullum face hidimta wa Nancy, ta hanyar dafa mata abinci mai dadi da gina jiki da tausa da taya ta motsa jiki.
Ana sa ran Nancy za ta haife cikin a ranar 5 ga watan Nuwamba, kuma dukkanin iyalan sun yi alkawarin karfafa mata gwiwa da kasancewa tare da ita a yayin haihuwar.
Tun bayan fitar labarin, ’yan uwa da abokan arziki da sauran mabiya a kafafen sada zumunta suka shiga jinjina wa Nancy kan irin kauna da soyayya da ta nuna wa danta Jeff.