Ta daure diyarta da sarka na tsawon kwanaki

Rundunar ’yan sandan kasar Ghana ta ceto wata yarinya ’yar shekara bakwai da mahaifiyarta da mijinta suka daure da sarka na tsawon kwanaki a wani kauye mai suna Dobidi na gundumar Kwahu da ke kasar. Yarinyar ta suma nan take bayan ’yan sandan sun ceto ta, inda daga nan aka garzaya da ita zuwa wani […]

Ta daure diyarta da sarka na tsawon kwanaki
Ta daure diyarta da sarka na tsawon kwanaki

Rundunar ’yan sandan kasar Ghana ta ceto wata yarinya ’yar shekara bakwai da mahaifiyarta da mijinta suka daure da sarka na tsawon kwanaki a wani kauye mai suna Dobidi na gundumar Kwahu da ke kasar.

Yarinyar ta suma nan take bayan ’yan sandan sun ceto ta, inda daga nan aka garzaya da ita zuwa wani asbitin gwamnati domin duba lafiyarta.
Kodayake, mahaifiyar yarinyar mai suna, Afua Annorbea da mijinta Kwasi Asante sun yi batan dabo.
Da yake karin bayani kan lamarin, jami’in ’yan sanda Cif Insfekta Seth Ehurem ya ce: “An ceto yarinya ne a rana Lahadin makon jiya, bayan wani mutum ya tsegunta wa rundunar sintirin da ke aiki a unguwar. Daga nan ne aka same ta daure cikin sarka a gidan”
Wasu mutanen kauyen sun shaida wa ’yan sanda cewa, “tsawon kwanaki uku yarinyar ta yi a daure cikin sarka bayan duka da azabtarwa iri-iri da mahaifiyarta da majinta ke gana mata.” Makwabtar sun bayyana cewa abin da ya sa yarinyar ta yi tsawon kwanaki a daure ba tare da sun bayya wa hukuma ba, shi ne sun ji tsoron abin da zai je ya dawo.
Mai magana da yawun ’yan sandan ya ce: “Za a ci gaba da bincike bayan an sallame ta daga asibiti domin gano irin laifin da tayi aka rika gana mata wannan azabar. Kuma jami’anmu sun bazama neman iyayen yarinyar wadanda suka tsere,” inji shi.