Ta dora alhakin karancin wutar lantarki a kan hukumar wutar lantarki taNERC

Cibiyar kasuwanci ta Jihar Legas wacce a takaice ake kira ‘LCCI’ ta ce bangaren samar da wutar lantarki na kasa bai tabuka abin arziki ba a shekarar 2014.Cibiyar ta ce kwararan hujjoji sun nuna cewa harkokin samar da wutar lantarki ya kara tabarbarewa a cikin shekarar da ta gabata.Shugaban cibiyar Remi Bello a rahotansa  na […]

Ta dora alhakin karancin wutar lantarki a kan hukumar wutar lantarki taNERC
Ta dora alhakin karancin wutar lantarki a kan hukumar wutar lantarki taNERC

Cibiyar kasuwanci ta Jihar Legas wacce a takaice ake kira ‘LCCI’ ta ce bangaren samar da wutar lantarki na kasa bai tabuka abin arziki ba a shekarar 2014.
Cibiyar ta ce kwararan hujjoji sun nuna cewa harkokin samar da wutar lantarki ya kara tabarbarewa a cikin shekarar da ta gabata.
Shugaban cibiyar Remi Bello a rahotansa  na tattalin arziki da ya gabatar na shekarar 2014, inda ya ce wutar lantarkin ta ragu da kashi 30 cikin 100 a bangaren kamfanoni da gidajen jama’a a shekarar 2014.
Bello ya bayyana cewa duk da ci gaban da aka samu na sayar da bangaren wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kansu ya ci gaba da kawo kalubale ga masu harkoki kasuwanci.
Ya ci gaba da cewa sun ci gaba da samun korafi daga bangarori da dama na yawan kudaden da suke kashewa saboda karancin wutar lantarki.
Ya shawarci hukumar lura da al’amaran wutar lantarki ta kasa NERC ta shigo cikin lamarin don yin maganin matsalar kudin wuta mai yawa da jama’a suke biya ba tare da samun wutar ba kamar yadda ya kamata.
‘A shekarar 2014 kananan kamfanoni sun yi korafin karin kudin wutar da ake yi musu inda suke kashe kashi 10 cikin 100 na abin da suke samu a wurin biyan kudin wutar lantarki, inda za ka ga irin wadannan kamfanoni ba sa samun wutar lantarkin da ake cewa su biya kudinta. Shi ya sa muke kara jadda cewa ya kamata a sake nazarin cajin kudin wutar da ake yi wa jama’a’. In ji shi.
Ya bayyana takaicinsa na jan kafar da ake yi a kan dokar kudurin man fetur, inda ya ce hakan yana yin tarnaki ga bunkasar harkokin man fetur da iskar gas.