Ta farfado daga doguwar suma bayan shekara 27

• Munira Abdulla, ’yar kasar Daular Larabawa hadarin mota ya rutsa da ita a 1991 • Sai da ta kwashe shekara 27 ba ta iya gane mutane • Tana fama da rauni a kwakwalwarta bayan bas din makaranta ta buge ta a ka, hakan ya sa ta sume • A bara ta fara magana, yanzu […]

Ta farfado daga doguwar suma bayan shekara 27

• Munira Abdulla, ’yar kasar Daular Larabawa hadarin mota ya rutsa da ita a 1991

• Sai da ta kwashe shekara 27 ba ta iya gane mutane

• Tana fama da rauni a kwakwalwarta bayan bas din makaranta ta buge ta a ka, hakan ya sa ta sume

• A bara ta fara magana, yanzu za ta iya tattaunawa da jama’a

Wata mata ’yar kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna Munira Abdulla mai shekara 32 da ta yi hadarin mota ta farfado bayan ta kwashe shekara 27 a sume.

Munira ta samu rauni a kwakwalwarta ce, lokacin da take tuki inda ta yi hadari da wata bas din makaranta a garin Al-Ain a 1991.

A bara ne a dakin asibitin da take jinya a kasar Jamus ta ji muryar danta mai suna Omar har ta yi yunkurin kiransa.

Duk a wadannan shekaru da ta yi a sume ba magana lokacin ne farkon fara furta wata kalma, a yanzu tana iya yin addu’a da kuma tattaunawa da ’yan uwanta.

Omar ya bayyana saukin da mahaifiyarsa Munira ta samu a wata tattaunawa da ya yi da jaridar The National inda ya nuna murnarsa na jin muryar da ya yi shekaru bai ji ba.

Omar ya bayyana yadda hadarin ya faru lokacin da yake shekara hudu, ya bukaci a dawo da shi gida daga makarantar yara, amma hakan bai yiwu ba saboda rashin samun motar bas din makarantar.

Dan uwan surukin Munira, ya tafi makarantar da Omar yake, don dauko shi, lokacin da suke tafiya a cikin motar tare da Munira da danta Omar don komawa gida, sai wata bas ta ci karo da motar da suke ciki.

A lokacin da hadarin ya faru, Munira ta yi kokarin kare danta daga raunin hadarin, hakan ya sa ta samu mummunan rauni a kanta. Omar ya samu raunuka kadan ne kawai.

Omar, ya bayyana cewa, a lokacin da mahaifiyarsa ta samu wannan mummunan raunin ba a yi mata magani na wasu sa’o’i ba, saboda ’yan uwanta a lokacin ba za su iya kiran masu agaji ba, kafin a kai ta asibitin Landan.

Likitocin sun yi wa Munira gwaji sun tabbatar da ba za ta iya tabuka komai ba, amma za ta iya jin zafin ciwo.

An dawo da ita kasar Daular Larabawa ne, inda aka sanya mata na’urar yin numfashi da bututun abinci da zai sanya ta rayu, duk wadannan shekarun da ta yi inji ke lura da ita.

A watan Afrilun shekarar 2017 Yariman Abu Dhabi Sheikh Mohamed bin Zayed, ya ji yanayin da Munira take ciki hakan ya sa ya ba iyalanta tallafin kudi don yi mata jinya a asibiti.

An kai Munira kasar Jamus don yi mata tiyata da maganin ciwon jikin da ke damunta da sauran magungunan da zai sauya barcinta.

A cikin shekara daya ta fara furta wasu kalmomi daga nan, sai kuma a cikin kwanaki uku ta kira sunan danta Omar.

Omar, ya ce “Mahaifiyata ta kira sunana, a lokacin na fara murna, kasancewar ina ta jiran wannan rana, kalmar sunana ta fara furtawa,” inji shi.

A yanzu Munira za ta iya kiran sunayen wadansu ’yan uwanta, za ta iya yin addu’a za ta kuma iya tattaunawa da jama’a.

A wani rahoton asibitin Mafrak da aka fitar watan jiya, ya ce yanzu haka Munira za ta iya tattaunawa da wadansu da ke tare da ita a cikin fahimta musamman ’yan uwanta. Duk da haka Munira tana bukatar wasu magunguna da za su taimaka mata.