Ta fim na samu damar kulawa da kaina- A’isha H. Umar

Aisha H. Umar na daya daga cikin sababbin ’yan fim masu tasowa a Jihar Kaduna,  ta shafe kusan shekara hudu a harkar fim. Ta ce ta fim ta samu damar kulawa da kanta sosai. Ba mu takaitaccen tarihinkiSunana A’isha U. Umar. Ni haifaffiyar Jihar Kaduna ce. Na fara karatun firamare a Sultan Bello da ke […]

Ta fim na samu damar kulawa da kaina- A’isha H. Umar

????????????????????????????????????

Jaruma A’isha H UmarAisha H. Umar na daya daga cikin sababbin ’yan fim masu tasowa a Jihar Kaduna,  ta shafe kusan shekara hudu a harkar fim. Ta ce ta fim ta samu damar kulawa da kanta sosai.

Ba mu takaitaccen tarihinki
Sunana A’isha U. Umar. Ni haifaffiyar Jihar Kaduna ce. Na fara karatun firamare a Sultan Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna. Bayan na kammala sai na koma sakandare da ke Dallat a Kawo, amma  ban kammala ba aka yi mini aure. Bayan mun rabu da mijin ne sai na shiga harkar fim. Yanzu haka na koma makarantar sakandare ta KTC domin ci gaba da karatuna.
  Me ya ba ki sha’awa har kika fara wannan sana’a?
Ina matukar sha’awar yadda ’yan fim ke isar da sako ta hanyar wayarwa da mutane kai a kan al’amuran da suka sha musu kai, kuma saboda ina so in rika  ba da tawa gudunmuwar sai na ga ya dace in fara wannan sana’a, domin in taimaka wajen wayar wa jama’a kai. Ina godiya matuka ga iyayena, domin sun ba ni ilimin addini daidai gwargwado. Amma abin da ya sa ba zan iya koyarwa ba shi ne ba ni da hakuri da yara. Ina fata da wannan sana’a tawa zan taimaka wajen ilmantar da jama’a.
  Kin yi kamar shekara nawa a harkar fim?
Yau kusan shekara hudu ke nan da na fara wannan sana’a.
 A cikin shekarun nan hudun da kika yi a harkar fim, kamar fina-finai nawa kika yi?  
Ba zan iya lissafasu ba domin suna da yawa, sai dai in lissafo maka kadan daga cikinsu. Akwai ‘Namamajo’ da ‘Mijin kanwata’ da ‘Ahlil Kitab’ da Tazuru’ da ‘Talaka’ da sauransu.
 A cikin fina-finan da kika yi wane kika fi so?
Na fi son fim din ‘Talaka’ duk da cewa na fito ne sau daya kacal a ciki. Fim din ne ya fito da ni fili har mutane suka san ni. Wannan shi ya sa na zabe shi. Na kuma yi rawar gani a cikin fim din ‘Mijin kanwata’.
 Ko za gi gaya mana rol din da kika hau a fim din ‘Talaka’ da ya kika fi sonsa?
 A fim din Umma Nolibu ce matar Ali Nuhu, inda ta matsa masa saboda ba shi da kudi, sannan kuma ga shi ta shiga adashi da muke yi. Bayan ta karbi nata sai ta ki zubawa, da na je karba sai ta ki ba ni, shi kuma mijinta na gida sai da na matsa masa ya ba ni kudin, ina tsammanin naira dari 5 na karba, sannan na bar shi da sauran naira ashirin. Irin rawar da na taka a fim din ne ya sa nake sonsa.
 Wani kalubale kike fuskanta a sana’ar fim?
Da farko dai iyayena ba su so na fara fim ba,  daga baya suka amince. Sun yarda cewa Allah ne ke yin yadda Ya so da dan Adam. Kuma duk abin da Allah Ya so mutum ya zama shi zai zama. Sai dai a kullum shawararsu gare ni ita ce, in tsare mutuncina kuma Alhamdullila na yi hakan.
  Tsawon shekaru nawa kike son yi a industiri?
Gaskiya ba zan ce ga shekarun da zan yi ba, domin mutuncin ’ya mace dakin mijinta. A yanzu muna nan a industiri amma fa da zarar na samu miji zan yi aure.
 Wane alheri kika samu a wannan sana’a ta fim?
Ina yi wa Allah godiya. Na samu alheri sosai idan aka gan ni da atamfa mai tsada ko takalmi, ko agogo ko wayar hannu mai tsada da sauransu duk ta hanyar fim na same su.
Kina nufin ba ki taba samun wadannan abubuwan ba sai da kika shiga sana’ar fim?
 A’a, abin da nake nufi shi ne,  ta dalilin fim na samu damar kulawa da kaina sosai. Amma kamar yadda na fada maka ne da farko cewa na shiga sana’ar fim ne kawai saboda in wayar da kan mutane.   
Wace shawara za ki ba mata masu sha’awar yin fim?
 Shawarata ita ce, su tsarkake niyyarsu, su sani Allah na kallonsu. Ga wadanda suke yin abin da bai dace ba kuma su ji tsoron Allah.