Ta gano mahaifiyarta bayan sun yi aiki shekara 4 tare
A makon jiya ne wata mata a Jihar Ohio ta kasar Amurka ta gano mahaifiyarta bayan sun yi aiki tare a wani kamfani na tsawon shekara hudu, ba tare da fahimtar hakan ba. Matar mai shekara 38, mai suna La-Sonya Mitchell-Clark, ta fara binciko sunan mahiafiyar ta ne daga takardun haihuwarta da Ma’aikatar Lafiyar kasar […]
A makon jiya ne wata mata a Jihar Ohio ta kasar Amurka ta gano mahaifiyarta bayan sun yi aiki tare a wani kamfani na tsawon shekara hudu, ba tare da fahimtar hakan ba.
Matar mai shekara 38, mai suna La-Sonya Mitchell-Clark, ta fara binciko sunan mahiafiyar ta ne daga takardun haihuwarta da Ma’aikatar Lafiyar kasar ta fitar na wadanda aka haifa tsakanin shekarar 1964 zuwa 1996, inda a ciki aka bayyana sunanta da Francine Simmons. Daga nan sai ta shiga shafin sada zumunta na Facebook, inda kaddamar da binciken sunaye kamar yadda kafar yada labarai ta Daily News ta bayyana.
Bayan samun sunan da ya dace da bincikenta, sai ta nemi bayanan game da wacce take zaton ita ce mahaifiyarta. Ta ce daga ne sai mamaki ya lulluveta bayan fahimtar cewa ma’aikaciyace a kamfanin da take aiki wato kamfanin sadarwa na InfoCision. “Amma abin da ya fi daure mini kai shi ne yadda muka yi aiki tare har na tsawon shekara hudu ba tare fahimtar hakan ba,” inji ta.
Har ila yau, La-Sonya ta gano cewa tana kanne mata uku, kuma guda daga cikinsu ita ma tana aiki a wannan kamfanin. Mai magana da yawun kamfaninya bayyana cewa “wannan abin mamaki ne.” Ya ce bana La-Sonya hudu take cika shekara hudu da fara aiki a wannan kamfanin, yayin da mahaifiyar take ciki shekara 10 da fara aiki da kamfanin a bana.
Francine ta ce ta haifi La-Sonya ne lokacin tana da shekara 14 a duniya, kuma an tilasta mata bayar da diyar da ta haifa sadaka. Wanda hakan ne ya yi sanadiyyar rabuwarsu.