Ta gurfana gaban kotu kan fasa idon dan masu haya

A ranar Talatar da ta gabata ne Kotun Shari’ar Musulunci ta Gyadi-Gyadi ta fara sauraron karar da ake zargin wata matar aure mai suna Murjanatu Sani da ke Unguwar Tarauni Masallaci a birnin Kano da tsiyaye wa wani yaro dan masu haya a gidan mai suna Idris Abubakar idonsa na dama.Takardar karar ta bayyana cewa […]

Ta gurfana gaban kotu kan fasa idon dan masu haya

Idris Abubakar yaron da aka tsiyaye wa idoA ranar Talatar da ta gabata ne Kotun Shari’ar Musulunci ta Gyadi-Gyadi ta fara sauraron karar da ake zargin wata matar aure mai suna Murjanatu Sani da ke Unguwar Tarauni Masallaci a birnin Kano da tsiyaye wa wani yaro dan masu haya a gidan mai suna Idris Abubakar idonsa na dama.
Takardar karar ta bayyana cewa “A ranar 5/12/2012 wani Abubakar Attahiru ya shigar da kara a ofishin ’yan sanda na Fam Santa cewa ke Murjanatu Sani kin yi amfani da bulogari da gangan ki ka jefi Idris Abubakar a ido wanda a dalilin haka idonsa na dama ya tsiyaye, kuma hakan laifi ne da ya saba da sashi na 159 na kundin shari’ar Musulunci ta shekarar 2000.”
Mai shari’a Habibudden Sulaiman Sharifai ya caji wacce ake zargi cewa in har laifin da ake zargin ta da shi ya tabbata, hukuncin biyan diyyar ido ya hau kanta, wato Naira miliyan 16 da dubu 404 da 165 da kuma daurin wata shida da bulala 20. Kamar yadda ke kunshe a sashi na 163 na dokar final kod.  
Sai dai wadda ake zargin ba ta amsa laifin ba, kuma kotun ta ba ta damar kare kanta a zaman kotun na ranar 11 ga watan gobe.
A ranar 5 ga Disamban bara ne Murjanatu ta jefi Idris mai kimanin shekara 10 da bulogari a ido lamarin da ya sa jini ya yi ta zuba daga idon yaron bayan an kwantar da shi a Asibitin Murtala idon ya tsiyaye.