Ta gutsure mazakutarsa bayan ya yi mata fyade

Wata mata mai suna Juaninta ’yar shekaru 24, ta gutsure mazakutar wani mutum wanda bayan ya yi mata fyade kuma ya nemi ta tsotsi gabansa. Lamarin ya faru ne jiya Asabar a Obuasi, yankin Ashanti na kasar Ghana yayin da mutumin ya shiga dakin matashiyar da tsakar dare kamar yadda Kakakin ’Yan sandan yankin ASP […]

Ta gutsure mazakutarsa bayan ya yi mata fyade

Wata mata mai suna Juaninta ’yar shekaru 24, ta gutsure mazakutar wani mutum wanda bayan ya yi mata fyade kuma ya nemi ta tsotsi gabansa.

Lamarin ya faru ne jiya Asabar a Obuasi, yankin Ashanti na kasar Ghana yayin da mutumin ya shiga dakin matashiyar da tsakar dare kamar yadda Kakakin ’Yan sandan yankin ASP Godwin Ahianyo ya bai wa manema labarai tabbaci.

Rahoton da BBC ya ruwaito ya ce mutumin mai suna Emmanuel Ankron mai shekaru 23, ya shiga dakin matashiyar wadda ta kasance daliba kuma ya nemi ta tsotsi mazakutarsa bayan ya yi mata fashi da makami wajen karbe mata dukiya.

A yayin da ta ke amsa bukatar Emmanuel ne Juaninta ta yanke shawarar gantsarawa mazakutarsa cizo da har ta kai shi ga kwanciya a gadon asibiti.

Ganin yadda jini ke tsiyaya daga gabansa ne ya santa ya tsere yayin da ita kuwa ta yi gaggawar kai kanta asibitin Anglogold Ashanti domin a duba lafiyarta.

Ana tsaka da duba lafiyarta ne a asibitin sai ga Emmanuel shi ma ya kai kansa asibitin inda cikin firgici ta gaggauta shigar da korafi kuma jami’an ’yan sanda suka yi ram da shi.

Binciken ’yan sanda ya gano gutsuren mazakutar matashin da Juaninta ta cizge da hakoronta yayin da ta ke tsotse masa gaba bayan ya yi mata fyade.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa