Ta hadu da diyarta bayan shekara 49 da sace ta

A ranar Alhamis din makon jiya ne wata uwa ta sanya diyarta a ido bayan bacewarta kimanin shekara 49 da suka wuce kamar yadda kafar yada labarai ta New York Daily News ta ruwaito. Matar mai suna Zella Jackson Price mai kimanin shekara 76 da take zaune a garin Olibette na Jihar Missouri ta kasar […]

Ta hadu da diyarta bayan shekara 49 da sace ta
Ta hadu da diyarta bayan shekara 49 da sace ta

A ranar Alhamis din makon jiya ne wata uwa ta sanya diyarta a ido bayan bacewarta kimanin shekara 49 da suka wuce kamar yadda kafar yada labarai ta New York Daily News ta ruwaito.

Matar mai suna Zella Jackson Price mai kimanin shekara 76 da take zaune a garin Olibette na Jihar Missouri ta kasar Amurka. Kuma an bayyana mata cewa diyarta ta rasu lokacin da ta haife ta a wani asibiti. Tun daga nan ba ta kara jin duriyar diyarta ba sai a makon jiya.
Zella ta ce wata ma’aikaciyar asibiti ce jim kadan bayan ta haihu ta shaida mata cewa diyarta ta rasu sakamakon bakwaini ce.
diyar wacce aka sanya wa sunan Melanie Diane Gilmore an bai wa wasu, inda aka shaida masu cewa iyeyenta sun ba da ita ne kyauta. A lokacin da ta kai shekara 20 ne bayan da aka bayyana mata abin da ya faru, sai Misis Melanie ta shiga neman iyayenta na asali.
Amma hakar ba ta cimma ruwa ba, sai a bara ’ya’yan Misis Melanie suka taimaka mata, inda suka gano kakarsu wato Zella ta amfani da shafin sada zumunta na Facebook. Kuma daga bisani gwajin kwayoyin halittan DNA suka tabbatar da hakan.
Misis Melanie wacce ta zama kurma tun tana da shekara uku da haihuwa, an sanar da ita labarin gano mahaifiyarta ta ce da yaren kurame, kafin daga bisani a sada ta da ita. Mahaifiyar ta ce: “Na gode wa Ubangiji saboda yadda Ya dawo mini da abin da shedanu suka raba ni da shi. Na same ta, na samu diyata.”
Daga nan ta bayyana aniyyarta na binciken hakikanin abin da ya faru domin gano mai laifi, ko ko hakan ya faru ne bisa kuskure. Ta ce: “Har yanzu ina cikin farin ciki. Ba za mu iya gane mai laifi ba, da abin da ya faru ba. Amma da zarar mun kammala wannan murna, zan dauki lauya,” inji ta.