Ta haifi jaririya tana cikin barci
Wata mai juna biyu ta haihu a lokacin da take tsaka da barci.
Wata mata ta bayar da wani labari mai ban mamaki kan yadda ta haihu tana cikin barci.
Matar ta wallafa wani bidiyo a shafin sada zumuntarta na TikTok wanda mutum sama da dubu 630 suka kalla.
- Sabon Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya ya kama aiki
- Za a yi wa Janar-Janar 30 ritaya bayan nada Faruk Yahaya
“Gaskiya abin tsoro ne, amma hakan ya yi daidai,” kamar yadda ta bayyana a tare da bidiyon kan yadda ta haifi jaririya a lokacin da take cikin barci.
Wani mai bin shafin a TikTok da adireshin @beyondboss_ ya tambayi mabiya shafin kan labarin yadda matar ta haihu wanda ya razana jama’a kan yadda ta haihu a cikin barci.
Wani mai sharhi mai suna Amy Dunbar da ya yi martani game da bidiyon, ya ce: “Wannan an yi ne don ni!”
A cikin bidiyon, Amy ya ce bayan sanya mata ruwan nakuda da awa 12 sai maganin ya sa ta fara yin barci ta kuma samu saukin ciwon jiki.
Bayan wani lokaci sai mai kula da lafiyarta ta dawo don duba ta, tare da kayan aikinta sai ta lura cewa tana da nauyin barci, hakan ya sa ta haihu a lokacin.
Amma matar ta ce, ba ta yi barci mai nauyi ba lokacin: “Bayan minti daya da haihuwar sai nas din ta tashe ni tana cewa ta rasa jaririyar saboda bugun zuciya kamar yadda na’urar kula da lafiyar ta nuna, amma ta ce, “Kada ku damu, zan yi bincike mai yiwuwa kawai jaririyar ta motsa ne.
“Ina yin abin da aka gaya min, na matsar da bargona ina jujjuyawa sai na kasance kamar ‘akwai wani abu da ke faruwa’.
“Jaririyata tana kan gado. Ta fitar da kanta yayin da nake barci. Lallai wannan babbar raguwa ce, ganin ungozoma da ta yi shi ne ta ji tsoro ta fito.”
A cikin bidiyon da ya biyo baya, ta ci gaba da cewa: “Ina kwance bayan na ja bargo a kan gado sai kawai mahaifata ta fita.
“Daga nan sai mahaifina ya fita daga cikin dakin yana yi ihu yana cewa, ‘Muna bukatar taimako!’
“Daga nan sai likitoci da nas-nas suka shigo dakin, amma kuma ba ta yin kuka,” inji ta.
Bayan likitocin jinyar sun duba jaririyar sai suka mika ta ga mai jegon sannan suka tabbatar da tana cikin koshin lafiya.
Amy ta ce, “Haihuwar abar tsoro ce, amma ba damuwa.”
Tun bayan wallafa bidiyon an samu mutum kimanin dubu 115 wadanda suka nuna sun burge su, mutum 2 ,200 suka yi sharhi.
Wani sharhi, cewa ya yi: “Jaririyar kamar ita ta yi kanta.”
Wani ya ce: “Wannan mace ce mai karfin dogaro da kanta.”
Yayin da wani ya ce, “Idan mace ta zo haihuwa ba abu ba ne na kuka, sai dai ta yi nishi mai karfi, idan jaririn ko jaririyar na cikin koshin lafiya, za su fito da kansu.”