Ta haifi tagwaye masu ubanni biyu
Wata kotu a Jihar New Jersey ta kasar Amurka ta umarci wani uba da ya biya ladan kula da daya daga cikin ’yan tagwayen da wata mata ta haifa, bayan wani kwaji da ya tabbatar da cewa tagwayen suna da ubanni daban-daban ne, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mirror ta bayyana. Wannan lamarin mai […]
Wata kotu a Jihar New Jersey ta kasar Amurka ta umarci wani uba da ya biya ladan kula da daya daga cikin ’yan tagwayen da wata mata ta haifa, bayan wani kwaji da ya tabbatar da cewa tagwayen suna da ubanni daban-daban ne, kamar yadda jaridar Birtaniya ta Daily Mirror ta bayyana.
Wannan lamarin mai daure kai ya kunno kai ne bayan wata mata wadda ta bayyana sunan ta da T.M ta bukaci tallafi daga hukuma, inda ta ce saurayinta ne uban tagwayen. Amma bayan da aka kai maganar a gaban kotu, an gudanar da binciki, kuma an fahimci cewa uwar tagwayen ta sadu da wani mutum a makon da aka yi amannar ta dauki cikin farko.
Har ila yau, bayan gudanar da binciken kwayoyin halittan tagwayen da na mazajen biyu da ake zargi, an tabbatar da cewa kowanne daga cikinsu uba ne ga daya daga cikin tagwayen wadanda yanzu haka sun fara rarrafe.
Alkalin kotun Sohail Muhammad ya ce wannan wani abu ne da ba a taba gani ba a duka fadin kasar Amurka.