Ta haifi ’yan hudu bayan shekara 18 tana neman haihuwa

              A ranar Asabar da ta gabata ne wata mata mai suna, Misis Clara Domikue ta haifi ’yan hudu a wani asibiti da ke birnin Benin na Jihar Edo, bayan ta kwashe shekara 18 tana neman haihuwa. Matar mai shekara 44, ta haifi jariran ne a wani asibiti mai […]

Ta haifi ’yan hudu bayan shekara 18 tana neman haihuwa

 

 

 

 

 

 

 

A ranar Asabar da ta gabata ne wata mata mai suna, Misis Clara Domikue ta haifi ’yan hudu a wani asibiti da ke birnin Benin na Jihar Edo, bayan ta kwashe shekara 18 tana neman haihuwa.
Matar mai shekara 44, ta haifi jariran ne a wani asibiti mai suna Graceland Medical Centre, inda ta haifi mata uku da namiji guda.
Misis Dominikue ta ce: “Na yi farinci matuka musamman ma saboda ni da mai gidana mun kasance tare har zuwa  wannan lokacin da Ubangiji ya nuna mana wannan rana. Mijina yakan karfafa mini gwiwa da cewa Ubangiji zai karbi addu’armu kuma bai taba tunanin ya rabu da ni ba. Mun yi aure ne a shekarar 1996.”
Ta ci gaba da cewa: “Lokacin da aka bayyana mini cewa ina dauke ne da ’yan hudu, a gaskiya na yi farin ciki matuka, amma nakan yi zullumin yadda zan dauke su su hudu lokaci guda saboda ban taba ganin wata wadda ta haifi ’yar hudu ba. Na sha wahala sosai lokacin da nake dauke da juna-biyun. A wadansu lokuta nakan ji cikin ya yi mini nauyi matuka.”
“Ni ce ke jagorantar yi wa jarirai addu’o’i kowace ranar Lahadin karshen wata a cocinmu. Hakazalika, ni ce na kan zama ta farko da ke fara ziyarta duk wadda ta haihu saboda in ba su kyautar abin da nake da shi, domin ni ba na damuwa ko kadan. ’Yan uwan mijina sun taba tsangwamata kan cewa ban haihu ba, amma sai mijina ya taka musu birki. Iyayena sun ta karfafa mana gwiwa. Wannan ne ya sa zamanmu ya dore,” inji ta.
Dokta Oni Samson wani likita ne  a asibitin  da Misis Dominikue ta haihu, kuma ya bayyana cewa ta haifi jariran ne bayan an mata aiki. Ya ce: “Ba zai yiwu ba a ce mace ta haifi yara da yawa ba tare da an yi mata aiki ba. Wannan shi ne karo na farko da muka samu ’yan hudu a wannan asibitin. A halin yanzu duka jariran  suna cikin koshin lafiya kuma suna karbar kulawa da gare mu,” inji shi.

 

 

 

 

 

 

 

Aminiya ta tuntubi Farfesa Abdullahi Muhammad, mataimakin shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmdu Bello da ke Shika Zariya, wanda kwararre ne a  fannin kimiyyar sanin cututtukan da ke damun dan adam (parasitology), domin sanin abin da ke sa mafi yawan irin wadannan jariran da aka haifa ba su dadewa, ko dai su mutu gaba daya ko kuma wadansu su mutu su bar wadansu, inda ya ce,’’ya danganta da irin filin da jariri ya samu a cikin cikin uwarsa ne, ka ga idan  sun kai takwas ma za su fito ne kamar ‘ya’yan beraye, amman girmar yaro shi yake nuna irin yawan kitsen da ke jikin yaron, sanyi ba zai saurin yi masa illa ba, amma idan ka ga yaro ba shi da girma, kitsen jikinsa ma ba shi da yawa,  saboda haka idan  kanana ne za ka gansu sai an sanya su a wata naura (incubator) da ke kawo dumi tare da iska (odygen), wato iskar da yaro ke shaka, kuma akwai abinci duk a cikinta, wato idan yaro yana cikinta kamar yana cikin mahaifiyarsa ne.’’
‘’A kasashe kamar Najeriya wannan na’urar ba mu da irinta da waya domin tsadarta, wadansu asibitocin ma ba su da ita, to idan aka sanya su a cikinta  za ka ga cewa sun fi rayuwa. Sannan kuma ciyar da su yana da mahimmanci, kila mahaifiyar ba za ta iya shayar  da su gaba daya ba, ka ga abincin da za a ba su ma sai kwararru sun ba su, sun kuma kula da su, ita ma mamar za ka ga cewa ba za ta iya shayar da su ba, in dai a nan Afrika ne, domin idan ka dube ta za ka ga ita kanta ma ba ta koshi ba yadda yakamata, balle ta kawo ruwan  nonon da za ta iya ba su su sha.’’
Ya ce, ‘’Duk da haka akwai wadansu dalilai, shi jaririn idan an haife shi kila ya zo da wadansu abubuwa a jikinsa, kamar makogwaronsa ko huhuhunsa wanda bai riga ya nuna ba sosai, saboda haka ba zai iya nunfashi ba sosai. idan a Turai ne ana dubawa a ga jaririn da bai yi kwari ba sosai, wato wanda huhunsa bai riga ya nuna ba, Turawa suna da yadda za su yi nan da nan sai su sanya musu abin da zai sa su su yi nunfashi da kyau,  su ba su magunguna, akwai magugunan da ake bayarwa da za su sa huhunsu ya nuna da wuri. To ka ga a nan wadannan na’urorin da magungunan akwai asibitocin ma da ba su da shi. Asibitocin koyarwa su ne yakamata a ce suna da su da yawa, duk da haka akwai wadansu kananan dalilai, amma dalilai sun fi goma zuwa talatin da za su sanya a ce jariri ya rayu.’’