Ta haifi yara 5 ringis a Ibadan
Wata mata mai suna Sakirat Alfa Yusuf Razak Ewenje ta haifi jarirai biyar a Asibitin Koyarwa na UCH da ke garin Ibadan a makon jiya. A ranar Litinin da ta gabata ce aka yi hudubar rada sunayen jariran uku maza, biyu mata.An rada wa mazajen jarirai 3 sunayen Ahmad da Muhammad da Mahmud, inda matan […]
Wata mata mai suna Sakirat Alfa Yusuf Razak Ewenje ta haifi jarirai biyar a Asibitin Koyarwa na UCH da ke garin Ibadan a makon jiya. A ranar Litinin da ta gabata ce aka yi hudubar rada sunayen jariran uku maza, biyu mata.
An rada wa mazajen jarirai 3 sunayen Ahmad da Muhammad da Mahmud, inda matan 2 aka sanya masu sunayen Amudat da Amudalat.
Hukumomin Asibitin UCH, inda matar ta haihu, sun tausaya, inda suka yafe kudin da ya kamata mijin mai jegon ya biya. Wato kudin magani da allurai na uwa da jariranta 5, na tsawon lokacin da likitoci suka yi suna kula da lafiyarsu a kan gadon asibitin.
Mai magana da yawun hukumar asibitin, Mista Deji Bobade, ya shaida wa wakilinmu cewa: “Hukumar zartarwa ta Asibitin UCH za ta mayar da dukkan kudaden magani da allurai da kwanciyar gado da ladar aiki, wanda Alfa Yusuf Rasak ya biya tun farko a matsayin cajin kudade da aka yafe masu tun daga ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu zuwa ranar da za a sallame su daga asibitin.”
Mahaifin jariran, Alfa Yusuf Rasak, dan shekara 32, wanda a can baya ya haifi ’ya’ya 2 da matarsa Sakirat, ’yar shekara 28 ya ce: “Tun lokacin da Sakirat take dauke da ciki na wata 3 aka dauki hoton da ya nuna cewa jarirai 5 take dauke da su a cikin mahaifarta, wanda muna sane da hakan tun daga wancan lokaci zuwa yanzu da ta haihu lami lafiya. A yayin da nakudar haihuwa ta fara tasowa, mun fara zuwa Asibitin Gwamnati na Adeoyo ne, inda suka tura mu zuwa Asibitin UCH, aka karbe mu da hannu biyu.”
Da yake tabbatar da labarin yafe masu kudaden da suka biya a asibitin, cewa ya yi: “Matata Sakirat, ita ce ta ba ni wannan labari mai faranta rai, cewa hukumar asibitin za ta dawo mana da dukkan kudaden da muka biya a baya kuma ba za su sake karbar ko kwabo daga hannunmu ba har zuwa lokacin da za a sallame ta daga asibitin. Na ji dadi kwarai da gaske da jin wannan labari.”
Ya kara da cewa: “Tun daga ranar da Sakirat ta haifi wadannan jarirai 5 zuwa yau, a kullum muna kashe kudi Naira dubu 18 zuwa dubu 25 domin sayen magani da allurai da ake yin amfani da su ga jariran da mahaifiyarsu.”
Da yake amsa wata tambaya, Alfa Yusuf cewa ya yi: “Babu wani bikin radin suna da muka yi a ranar Litinin da jariran suka cika kwanaki 7 da haihuwa, sai dai mun yi masu hudubar radin suna kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. A wannan rana, ba na tare da su, ina can uzurin gabana ya ishe ni wajen sayen magunguna.” Ya mika rokonsa ga kamfanonin harhada magani da su taimaka wa iyalinsa da irin magungunan da ake bukata domin ceton rayukan jariran. Haka kuma ya mika kokon bara ga Gwamna Abiola Ajimobi da matarsa Florence da su tallafa masa.