Ta haifi ‘ya’ya 5 a haihuwa 2 bayan shekara 10 babu haihuwa
Wata mata mai suna Maryam Abubakar, ‘yar shekara 24 ta haifi yara hudu maza a asibitin (Primary Health Care) da ke layin Sarki a Tudun Wada Zariya . Ita dai wannan mata wadda take zaune a ‘yan kifi Kwanar dangoma gundumar Tukur-Tukur a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna. Aminiya ta ziyarci wannan mai jego domin […]

Wata mata mai suna Maryam Abubakar, ‘yar shekara 24 ta haifi yara hudu maza a asibitin (Primary Health Care) da ke layin Sarki a Tudun Wada Zariya .
Ita dai wannan mata wadda take zaune a ‘yan kifi Kwanar dangoma gundumar Tukur-Tukur a karamar hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
Aminiya ta ziyarci wannan mai jego domin jin yadda ta ji a lokacin da take dauke da cikin har zuwa haihuwarsu, inda ta ce, ‘’ To a gaskiya bambancin da na ji a wancan ciki na farko da wannan shi ne nauyin da kuma girmar cikin,domin wannan ita ce haihuwata ta biyu. Na farko na haifi da namiji, bayan shekara uku sannan kuma Allah Ya ba ni wadannan dama ni ba na wasa wajen zuwa asibiti da na samu juna biyu, domin zuwa wurinsu zai taimaka mun. Don haka ko da na samu wannan cikin ban yi wasa ba wurin zuwa awo, kuma asibitin da ya fi kusa da mu irin wadannan kananan su nake zuwa ana duba ni akai-akai, kuma na cika dukkan ka’idoji da yakamata mai awo ta yi, kamar hoto na ciki da dai sauransu. Hoton ya nuna yara biyu zan Haifa, don haka duk irin tanadin da za mu yi na yara biyu muka yi. Da nakuda ta kama ni ban zauna a gida ba, na garzaya zuwa asibiti inda su ma’aikatan suka kwantar da ni kuma suka ba ni kulawar da ta dace. Da misalin karfe 4 na dare sai na haifi da na farko, bayan wani lokaci kuma na kara haihuwa. To ni a zatona na gama, sai ma’aikatan jiyyar suka ce akwai sauran daya, bayan lokaci na haihu suka kara ce min akwai saura kuma, na cika da mamaki, domin dukkansu ban sha wahala ba,na haihu lafiya lau.Bayan Allah Ya sa na haihu sai ma’aikatan suka ce ai maza ne duka na Haifa. Daga nan sai ita babbarsu ta ba da takarda tare da ba mu umarnin da mu je babban asibitin da ke Shika. Ka ji dalilin zuwanmu nan ke nan. Amma fa tun da muka zo sun karbi yaran suka sanya su a cikin kwalba, har yau ni ban taba ko daya daga cikinsu ba, sai dai kawai inje in kale su, ko da nono ban ba ko daya a cikinsu ba. Amma ni lafiyata lau ba ni da wata larura.
Wakilinmu ya kuma tuntubi mahaifin yaran mai suna Abubakar, domin jin yadda ya yi da aka ce matarsa ta haifi yara hudu, inda ya ce, ‘’ to na farko dai na yi wa Allah godiya, kasancewar shi ne ya yi mun wannan kyauta, domin a lokacin da na auri matata Maryam sai da muka shekara goma Allah bai ba mu haihuwa ba, a inda daga baya muka haifi da namiji, bayan shekara uku ne da haihuwar na farkon sai kuma Allah Ya ba mu wannan kyauta na haihuwar ‘ya’ya 4 maza gaba daya, kuma mu mun dauka yara biyu ne za ta Haifa, domin hoton da muka yi na awon ciki da ake yi ya nuna yara 2 ne, ashe Allah Ya yi ikonSa, wanda babu wanda ya isa ya sani sai shi, sai ga yara hudu,ina wa Allah godiya.
Kuma kamar yadda ka tambayi irin sana’ar da nake yi, to ni ina kabo-kabo ne da mota kirar golf, wannan ita ce sana’ata, kuma Allah bai hana ni yadda zan dauki nauyin iyalina ba kafin wannan kyauta da ya yi mun, sai dai yanzu na fara gazawa, domin duk tanadin da na yi ya wuce a harkar asibiti wajen kula da wadannan yara hudu, domin daga lokacin da muka zo zuwa yau kwananmu hudu ke nan, amma na kashe kudi ya kai Naira dubu 60, tsakanin magani da abinci, kusan duk abin da nake yi ma na daina, domin da na dan fita sai ka ji kira a waya cewa ana nemana a sayi wani abu, yanzu ‘yan uwana da abokanaina suke tallafa mun da kuma wadanda suka ji cewa matata ta haifi yara 4. Baya ga haka kuma yanzu da na ji matata ta kira ni a waya sai gabana ya fadi,domin na san wani abu za a nema, don haka nake rokon Allah da Ya ba ni wadanda za su taimaka mun wajen dawainiyar asbibitin nan kawai, idan ya so sauran na yau da kullum Allah zai ba mu, amma wannan na Asibitin shi yake damuna,domin a ce ka kawo babu, ba dadi. Domin tsakanin magunguna da abin da ake ba su a madadin nono da kuma kudin da nake biya na cikin wurin da aka sanya su su ne suke datsada, don haka nake bukatar a taimaka mun wajen kula da lafiyarsu.
Aminiya ta garzaya asibitin da aka haifi yaran a Tudun Wada Zariya inda ta sadu da babbar jami’ar da ta karbi haihuwar don jin yadda ta yi, inda ta ce.’’ Sunana Zulaihatu Muhammad kuma ni ina aiki a nan ne, wannan mata mai suna Maryam an kawo ta tana nakuda muka karbe ta muka kwantar da ita, ganin yadda haihuwar ta taso mata gadan-gadan, misalin karfe 4 na asuba sai ta haifi yaro na farko, bayan minti 40 ta haifi na 2, bayan minti 30 ta kara haihuwar na 3, tsakanin na 3 da na 4 minti goma ne kawai, don haka ta haifi yaran ne gaba daya cikin awa daya da minti 40. Yaro na farko nauyinsa keji daya ne, na 2 kuma yana da keji 1 da digo 2, na ukun kuma yana da keji daya da digo 3, na karshen shi kuma yana da nauyin keji daya kamar na farko. Kuma a gaskiya dukkansu sun dan yi kuka kada-kadan a lokaci da aka haife su, kuma numfashinsu ba yafita sosai yadda ake bukata, kuma ga shi nauyinsu babu wanda ya kai yadda ake so, don haka na rubuta takarda na ba su na tura su babban asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin su suna da kayayyakin da ya dace da kuma kwararrun likitocin da za su iya kula da lafiyar yaran kamar yadda ya dace. Kuma ina kira ga mata da su rika kokarin zuwa awo idan suna da juna biyu, kada su yadda su ce za su zauna a gida idan nakuda ta kama su, domin yin awo zai sa a gane halin da ita mai ciki da kuma dan da ke cikin suke ciki.
Wani likita da bai so a bayyana sunansa ba wanda Aminiya ta same shi a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello yana kula da wadannan yara, ya ce yaran sun yi kakanta kwarai kuma numfashinsu yakan yanke lokaci bayan lokaci, don haka muke ba su kulawa ta musamman,kuma ba mu bukatar kowa ya je inda suke, sai dai mahaifan yaran, su ma don su gansu ne, domin hatta abincin da yaran suke bukata mu muke ba su. Sai dai ita uwar lafiyarta lau, ba ta da wata matsala.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton yaran duk su hudu suna nan a raye.