Ta haihu a hannu masu garkuwa da ita bayan sa’o’i 5 a Zamfara
Rahotanni na cewa, wata mata ta haihu bayan sa’o’i 5 da yin garkuwa da ita a Kauyen Danjibga da ke Karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. A lokacin da masu garkuwan suka shiga garin sun yi yunkurin tafiya da wani dan kasuwa amma Allah ya bashi dama ya tsere ya bar matansa biyu a gida, […]
Rahotanni na cewa, wata mata ta haihu bayan sa’o’i 5 da yin garkuwa da ita a Kauyen Danjibga da ke Karamar Hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
A lokacin da masu garkuwan suka shiga garin sun yi yunkurin tafiya da wani dan kasuwa amma Allah ya bashi dama ya tsere ya bar matansa biyu a gida, daya daga ciki na shirin haihuwa amma suka tafi da mai cikin bayan ta haihu a hannunsu sai suka kira mijin suka sanar da shi cewa, matarsa ta haihu.
A ranar juma’a da ta gaba ta ne wasu da ake zargin barayin shanu ne suka shiga kauyen suka kwashe shanu 17 tare da kashe mutum uku da kuma yin garkuwa da wani mutum daya. Kamar yadda wani mazaunin garin da baiso a bayyana sunansa ba ya sanarwa majiyarmu