Ta halaka kanta da mijinta a kan kishiya
Shekarar 2014 ta zo wa iyalan gidan Monday da ke kauyen Amobo a karamar Hukumar Mbaise ta jihar Imo da rudani, inda a ranar 11 ga watan Janairun nan wata matar aure mai suna Misis Ngozi Monday ta watsa wa gidansu mai dakuna bakwai fetur kuma ta kira mijinta cikin dakinta ta banka wa gidan […]

Shekarar 2014 ta zo wa iyalan gidan Monday da ke kauyen Amobo a karamar Hukumar Mbaise ta jihar Imo da rudani, inda a ranar 11 ga watan Janairun nan wata matar aure mai suna Misis Ngozi Monday ta watsa wa gidansu mai dakuna bakwai fetur kuma ta kira mijinta cikin dakinta ta banka wa gidan wuta, gaba dayan gidan ya kone kurmus tare da su.
Ita dai Ngozi ta auri mijinta Monday ne shekaru 16 zuwa 17 da suka gabata, amma Allah bai sanya ta samu haihuwa ba, saboda tsananin damuwa ta yi sai ta yi alkawarin haifar da bala’i ga wannan gida nasu matukar mijinta ya kara wani auren.
Kafin rasuwarta an shirya za ta je gidan da ‘yarta ta haihu (wadda ta haifa kafin ta yi aure) ne domin ta taimaka mata wajen renon jaririyar da ta haifa, ‘’ashe ba a sani ba ta ki tafiya can saboda tana da wani mugun kulli a zuciyarta,’’ inji wani daga cikin iyalan gidan.
Mista Chinedum dan shekara 40, kani ne ga marigayi Monday, ya bayyana wa wakilinmu cewa, tun da marigayi Monday ya auro wata matar har ta haifa masa ‘ya’ya biyu mata, Ngozi take ta gunaguni tare da yin barazana saboda ba ta amince da kara auren da ya yi ba.
Ya bayyana wa Aminiya cewa, ‘’a ranar asabar da misalin karfe 12 ko 1 na rana ina rumfata a kasuwa inda nake dinki, sai wani yaro ya zo a guje ya ce mini in zo da sauri gidanmu na cin wuta, na ce masa wutar lantaki ce ta jawo wutar? Ya ce bai sani ba. Sai na nemi abin hawa amma da ban samu ba sai na hau keken da yaron ya zo da shi, ina isa sai na tarar da gaba dayan gidan yana cin wuta.
A cewar Chinedum, duk kokarin da ya yi na shiga gidan domin ya kashe wutar ya ci tura saboda wutar ta kama sosai. Ganin cewa babu abin da zai iya yi domin kashe wutar ko ya fitar da wani kaya daga gidan, sai ya shiga neman motar da za ta kai dan uwansa asibiti ko zai iya rayuwa, domin a lokacin yana iya magana.
Chinedum ya ci gaba da cewa, ya kai wa ‘yan sanda rahoto a ofishinsu da ke Itu, wadanda nan take suka je suka gane wa idanunsu abin da ya faru har ma suka samu wadansu bayanai a wurin dan uwansa marigayi Monday kafin ya cika a asibiti.
Ya ce, ya ji dan uwan nasa yana fada wa ‘yan sanda cewa, ‘’yana cikin rumfa lokacin da matarsa Ngozi ta kira shi, yana shiga gidan sai ya ji warin fetur, inda ya yi mamakin abin da ya kawo warin fetur a gidan, sai matar ta ce masa ya shigo cikin daki, yana shiga cikin dakin sai ya ji ta kyasta laitar da ke hannunta. Ya ce bai san yadda aka ya iya fita waje ba. Yana cikin bayanin ne sai ya kasa, daga nan ya cika.’’ inji Chinedum.
Da aka tambaye shi ko Ngozi, wadda take sayar da injin oyel, daga baya ta bude wurin sayar da abinci, ta taba yin wani korafi, sai Chinedum ya ce ba ta taba ba, amma ya san a tsawon shekara 16 zuwa 17 da suka yi da aure ba ta taba haihuwa ba, ‘’saboda haka sai mijin nata ya kara auren wata matar, kuma tun lokacin ta nuna bacin ranta. An rabu da ita za ta je ta taimaka wa ‘yarta renon jaririyarta ne, domin tana da ‘ya da haifa a gidan iyayenta kafin ta yi aure, maimakon ta je ta taimaka wajen renon, dubi abin da ta yi wa iyalinmu.’’
Da wakilinmu ya je asibitin St. Peter da ke Ezeagbogu mai nisan kilomita kusan hudu daga inda al’amarin ya faru, inda aka kai Monday, likitan asibitin Dokta Bimbo Olufeaba ya bayyana masa cewa, ’’lokacin da aka kawo Monday yana iya magana, duk da cewa ya kone sosai har ya makance, lebbensa sun fara mannewa saboda zafin konar, gashin kansa duk ya kone. Sai na ce musu su wuce da shi zuwa asbitin tarayya da ke Owerri, amma sai suka yi ta rokona in duba shi, bana son karbarsa ne saboda na fahimci da wuya ya rayu, amma da ‘yan uwansa suka matsa sai na karbe shi na fara duba shi domin ya samu saukin mutuwa.’’
Likitan ya ci gaba da cewa, jami’an ‘yan sanda, watau DPO da DCO na yankin duk suna asibitin lokacin da Monday ya cika.
Sai dai kuma wata kawar Ngozi ta bayar da bayanin da ya bambanta da na dan uwan marigayi Monday, inda ta ce, ‘’lokacin da mijinta ya kara aure sai ta fara shaye-shaye tare da bin maza, mijin nata sai ya gargade ta, har ma a wani lokaci a makon da ya gabata ya kwashe ta da mari saboda muguwar dabi’ar da ta fara, ita kuma sai ta yi alkawarin ramawa ta mummunar hanya.’’
Ngozi dai ta kone kurmus daga wutar da ta kunna da hannunta, lokacin da wakilinmu ya je gidan ya tarar da dimbin mutane a gidan wadanda suke je domin yin jaje, kuma har zuwa lokacin gawar Ngozi na nan a cikin wani daki.
Da wakilinmu ya tafi ofishin ‘yan sanda ya tarar jami’in ofishin (DPO) ya tafi Owerri domin ganawa da kwamishinan ‘yan sanda, shi kuma mataimakinsa ya ki cewa uffan game da al’amarin, saboda ya ce ba a ba shi ikon yin magana da manema labarai ba. Amma wata majiya ta ‘yan sanda da ke ofishin ta tabbatar da faruwar lamarin.
Mutanen garin dai suna ta yin tofin Alla-tsine ga Ngozi, wadda suka ce da ta kashe kanta ita kadai kawai, maimakon jefa mutane 15 da ke cikin gidan cikin halin kaka-ni-ka-yi. ‘’Idan da ta kashe kanta tare da mijin nata ne kawai sai a ce da sauki, amma banka wa gidan gaba daya wuta da ta yi ya wuce iyaka, kuma hauka ne,’’ inji wata da ta je jaje. Wata kuma cewa ta yi, ‘’wannan matar ta fara cin wutar jahannama tun daga nan.’’
Chinedum dai ya roki gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha da shugaban karamar hukumar Ezinihitte da kuma sauran jama’a da su taimaka musu.
Abubakar Haruna, Daga Legas
Wata mata mai yawon bara da tagwayen da ta haifa a jihar Legas, mai suna Shakirat Olariwaju ta ce tana yin bara da ’ya’yanta ne saboda tsoron kada su mutu.
Shakirat ’yar asalin garin Abeokuta da ke jihar Ogun, wacce ba ta jin harshen Turanci, ta bayyana wa Aminiya ta hanyar tafinta cewa ta yi asarar tagwayenta su hudu saboda kin yin bara da su.
Ta ce, ‘Na haifi ’yan biyu har sau biyu amma sun mutu saboda mutanenmu sun umarce ni in yi bara da su amma sai na ki, saboda haka suka kamu da rashin lafiya suka mutu. Da na haifi wadannan su ma sai suka kamu da rashin lafiya. Sai masu magani suka ce dole sai na yi bara da su sannan za su samu lafiya, idan ba haka ba su ma za su mutu. Kafin in fara bara da su ba sa yin magana kuma ba sa tafiya, duk da cewa sun kai shekaru biyar da haihuwa amma da na fara bara da su har Taye ya fara magana shi kuwa Kehinde ya fara tafiya.’
Ta ci gaba da cewa, ‘A da ban yarda da wannan al’ada ba saboda ni Kirista ce, amma yanzu da na gwada na gani na yarda na amince dari bisa dari cewa idan Allah ya ba ka tagwaye dole sai ka yi bara da su idan ba haka ba za su mutu ko kuma su nakasa. Saboda haka zan ci gaba da yin bara da su har sai sun samu lafiya, sun mike suna tafiya kuma suna magana sannan zan daina bara da su.’
Shakirat ’yar kimanin shekara 27 da haihuwa, ta dage a kan cewa ba talauci ba ne ya sa ta yin bara da tagwayenta, domin mijinta kafinta ne wanda yake da rufin asiri: “Ba don talauci nake yin bara da su ba saboda mijina yana da sana’a. Sana’ar kafinta yake yi, yana da rufin asiri. Kuma mun kai su asibiti mun kashe kudi sosai amma yaran ba su samu lafiya ba, shi ya sa muka yanke shawarar mu bi abin da aka gaya mana.’ Inji ta.
Ta bayyana cewa, da zarar ta kammala yawon bara da su za ta kama sana’ar saye da sayarwa kamar yadda ta saba.
Mijinta mai suna Olariwaju wanda bai yarda a dauki muryarsa ko hotonsa ba, ya bayyana cewa ya kyale matarsa ta yi bara da ’ya’yansa saboda bin umarnin da masu maganin gargajiya suka ba su.
Ya bayyana cewa, ba a kan tagwayensu aka fara bara da tagwaye a kasar Yarabawa ba, saboda al’ada ce da suka gada iyaye da kakanni.
Wani mai suna Femi da ya ba ta sadaka, ya bayyana cewa ya ba ta sadakar ne saboda Allah ba don abin da zai samu daga tagwayen ba.
Ya bayyana cewa wadansu masu ba ta sadaka sun yi imanin cewa tagwayen za su iya sa wa su samu nasara a harkokinsu na yau da kullum. “Shi ya sa kake ganin suna ba ta sadaka saboda wadansu Yarabawa sun yi imanin cewa tagwaye suna da wata albarka ta sa wa ka samu nasara ko akasin haka a harkokin yau da kullum, amma ni ban yi imani da haka ba a matsayina na musulmi.” Inji shi.
Wani mai maganin gargajiya mai suna Baba Papoola ya bayyana cewa ana haihuwar tagwaye da matsaloli daban-daban.
“Wadansu sai an yi bara da su sannan a samu waraka, wadansu kuwa sai an rika yi musu dafe-dafe da yanke-yanke sannan za su bari iyayensu su samu ci gaba. Ita ta yiwu an gano suna dauke da wadansu aljanu shi ya sa aka umarce ta ta yi bara da su. Al’ada ce da muka gada iyaye da kakanni.”
Wani malamin addinin musulunci mai suna Alfa Alaka ya yi watsi da lamarin, inda ya ce musulunci bai umarci cewa sai an yi bara da tagwaye ba sannan za a samu wani abu: “Babu inda a musulunci a ka ce tagwaye suna cutarwa kuma babu inda aka ce sai ka yi bara da su sannan za ka samu wata waraka. Mutane ne suka yi imani da haka shi ya sa shaidan yake jan hankalinsu. Idan suka yi imani da Allah babu abin da zai samu tagwayen tare da su.’
Fasto Tunde Adeleke na cocin Cele da ke Ikeja ya bayyana cewa al’ada ce ta wadansu Yarabawa amma ba littafin Baibul ba ne ya yi umarni da a yi bara da tagwaye ba.
Yarabawa da yawa da Aminiya ta tattauna da su kan lamarin sun kasu biyu, wadansu sun goyi bayan lamarin, wadansu kuma ba su goyi bayan dole sai an yi bara da tagwaye ba za su samu lafiya.
Wannan al’ada ta yi kama da ala’dar wadansu Hausawa da ke yin bara da tagwaye don kada su cutar da iyayensu ko kuma su samu wata nakasa a rayuwarsu.
Wadansu Hausawa sun yi imanin cewa tagwaye suna da wata albarka ta musamman shi ya sa suke yi musu kirari da cewa ’Yan biyu kyautar Allah.’
Wadansu kuma sun yi imanin cewa tagwaye suna yi wa mutum kofi ko kwari ya rika ganin maciji ko kunama ko kuma idan aka bata musu rai sai abinci ya ki dahuwa.