Ta hallaka budurwar tsohon saurayinta ta kona gidansa

’Yan sanda sun cafke ta bayan ta banka wa gidan wuta a lokacin da budurwarsa ke ciki.

Ta hallaka budurwar tsohon saurayinta ta kona gidansa

Wata Gobara

’Yan sanda sun cafke wata budurwa da kawarata bisa zarginsu da kashe budurwar tsohon saurayinta da kuma kona masa gida.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Legas, Olumuyiwa Adejobi, ya ce kama ’yan matan ne bayan sun kona gidan tsohon saurayin a Monkey Village da ke unguwar FESTAC a jihar.

“’Yan sandan sun kama ta da kawarta da ta taimaka mata suka aikata laifin kuma Kwamishinan ’Yan Sanda ya bada umarnin a mayar da su Sashen Binciken Manyan Laifuka”, inji Adejobi.

Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewar a ranar 18 ga watan Nuwamba ne budurwar da kawarta suka je gidan tsohon saurayin inda budurwarsa ke ciki suka kuma cinna masa wuta.

An ce, bayan ya samu labarin abin da ya faru ne ya garzaya gidan inda ya ciro budurwar tasa mai suna Rabi daga ciki amma ta rasu bayan ya kai ta asibiti.

Majiyar ta ce Yusuf ya rabu da tsohuwar budurwar tasa ce saboda zargin ta da rashin kamun kai.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya gargadi mutane da sun guji daukar doka a hannunsu saboda Rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an hukunta duk wanda ta kama da laifi.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7