Ta ja daga da mijinta kan amfani da mahaifarta domin tsafi

Gardama ta murtuke a tsakanin wata mata mai suna Opeyemi da mijinta mai suna Ademola Adelanwa, wanda ta ce ya lallabe ta domin yin amfani da mahaifarta a yi tsafin samun kudi cikin dare daya, amma ta ki amincewa. Haka kuma, ta tabbatar da zargin sace ’yan kamfayenta kan mijin nata, domin yin amfani da […]

Ta ja daga da mijinta kan amfani da mahaifarta domin tsafi
Ta ja daga da mijinta kan amfani da mahaifarta domin tsafi

Gardama ta murtuke a tsakanin wata mata mai suna Opeyemi da mijinta mai suna Ademola Adelanwa, wanda ta ce ya lallabe ta domin yin amfani da mahaifarta a yi tsafin samun kudi cikin dare daya, amma ta ki amincewa. Haka kuma, ta tabbatar da zargin sace ’yan kamfayenta kan mijin nata, domin yin amfani da su wajen tsafin.
Uwargida Opeyemi tana fadin haka ne domin kare kanta a gaban wata kotun gargajiya da ke Ibadan, inda mijinta ya nemi a raba aurensu na shekaru 11, saboda yawan karairayi da bata sunansa a gaban iyayensa da surukansa da makwabtansa har da cocin da suke zuwa take yi masa.
“Tuntuni na daina zuwa cocin kuma na kaurace wa gidan zuriyarmu da muke zaune tare da ita, saboda karyar da take yi tana bata mini suna. Ta taba zargin na sace mata kamfayenta, amma Allah ya tserar da ni, ta gano inda ta boye kayanta. Kuma, fitinanniyar mace ce, ta sha cukuma ta da fada a gaban mutane, ta hana ni sakat, balle in ji dadin zaman aure. Na yi yunkurin rabuwa da ita, amma saboda wasu dalilai na hakura, sai dai yanzu tura ta kai bango, shi ya sa na zo kotu domin a raba auren namu kowa ya kama gabansa”. Inji Mista Ademola.
Don kare kanta a gaban kotun, Uwargida Opeyemi ta ce gaskiya ne ta zargi miji nata game wadannan al’amura, “Amma ina rokon kada kotu ta amince da bukatar a raba aurenmu, saboda na san yana cikin wasu matsaloli kuma ni ba zan sake yin wani aure ba”.
Bayan sauraron bayanansu, shugaban kotun, Mai shari’a Amusa Makinde ya ba su wa’adin mako biyu su koma gida su sake zama da iyaye domin sasantawa, musamman ganin akwai alamun soyayya da kauna a tsakaninsu.