…Ta kafa kwamitin bincikar zargin cin zarafi da Sanata Elisha ya yi ga wata mata
Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamitin mai mutum 7 da zai binciki zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sanata Elisha Abbo Cliff na PDP daga Mazabar Adamawa ta Arewa. Wani faifan bidiyo da kafar labarai ta Premium Times ta saki ya nuna yadda Sanata Elisha Abbo yana cin zarafin wata mata a […]
Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamitin mai mutum 7 da zai binciki zargin cin zarafin wata mata da ake yi wa Sanata Elisha Abbo Cliff na PDP daga Mazabar Adamawa ta Arewa.
Wani faifan bidiyo da kafar labarai ta Premium Times ta saki ya nuna yadda Sanata Elisha Abbo yana cin zarafin wata mata a wani shagon sayar da kayayyakin jima’i a Abuja. Faifan bidiyon an ta yada shi a kafofin sadarwa na zamani tun a ranar Talatar da ta gabata.
Da yake gabatar da batun gaban majalisar, Sanata Uba Sani (APC, Kaduna), ya ce hakika wannan lamari ya bata wa majalisar suna, inda ya ce akalla ya samu kiraye-kiraye a waya daga ciki da wajen kasar nan fiye da 111 kan lamarin. Ya ce wannan babban abin kunya ne ga majalisar. Kudirin ya samu goyon bayan Sanata Opeyemi Bamidele daga Jihar Ekiti.
Shugaban Marasa Rinjaye Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce majalisar na da dokokinta kuma dole ne kowane dan majalisa walau a majalisar ko a wajenta ya kasance mai bin dokar.
Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Abdullahi Yahaya daga Jihar Kebbi ya goyi bayan kafa kwamitin binciken, saboda akwai bukatar majalisar ta dauki mataki a kan lamarin.
Shugaban Majalisar, Sanata Ahmed Lawan ya ce duk abin da aka gani a kafofin sadarwa ko aka karanta kan lamarin yana zaman zargi ne, sai an gudanar da bincike a kansa. Nan take ya kafa kwamitin a karkashin jagorancin Sanata Samuel Egwu (PDP, Ebonyi). Sauran ’yan kwamitin su ne Oluremi Tinubu (APC, Legas) da Matthew Urhoghide (PDP, Edo), Stella Oduah (PDP, Anambra), Mohammed Sani Musa (APC, Neja), Danladi Sankara (APC, Jigawa) da Halliru Dauda Jika (APC, Bauchi), kwamitin na da mako biyu don ya kammala aikinsa.