Ta kai gawar wani ya sa hannu ta samu lamuni a banki
A zahiri bai nuna alamun yana dai rai ba, amma Vieira Nunes ta ci gaba da gaya wa ma’aikatan cewa dattijon ya yi shiru ne kawai.
A kwanakin baya ne aka kama wata ’yar ƙasar Brazil mai shekara 42 bisa zarginta da kai wani matacce cikin banki tare da ƙoƙarin karɓar lamuni a bankin da sunansa.
A ranar 16 ga Afrilu 2024, matar mai suna Erika de Souza Vieira Nunes ta isa reshen Bankin Itau Unibanco a yankin Bangu, da ke Jihar Rio de Janeiro don taimaka wa dattijo mai suna Paulo Roberto Braga mai shekara 68 samun lamunin banki da ya kai Dalar Amurka 3,200 (kimanin Naira miliyan 3 da dubu 442).
- An tsinci gawar wata ɗaliba a cikin ɗaki a Kano
- Hisbah ta ware wa ’yan jarida gurbi 50 a auren gata — Daurawa
Dattijon yana kan keken guragu ne kuma ta yi iƙirarin cewa ita ’yar dan uwansa ce kuma mai kula da shi.
Sai ma’aikatan bankin suka lura cewa akwai wani abu mai tsanani a tattare da dattijo Braga, domin ’yar uwarsa tana riƙe kansa da hannunta.
A zahiri bai nuna alamun yana dai rai ba, amma Vieira Nunes ta ci gaba da gaya wa ma’aikatan cewa dattijon ya yi shiru ne kawai har ta yi ƙoƙarin yi masa magana duk da a fili bai iya ba da amsa ba.
“Kawu kana ji? Kana buƙatar sanya hannu. Idan ba ka sanya hannu ba, babu wata hanya,”
Shaidu suka ji Erika de Souza Vieira Nunes tana gaya wa mutumin da ke kan keken guragu (alhali gawa ce).
“Ba zan iya sa hannu a madadinka ba, abin da zan iya yi zan yi. Sa hannu a nan, daidai da takardar. Sa hannu don kada ka ƙara min ciwon kai,” in ji ta.
A wani lokaci, ana iya jin ɗaya daga cikin ma’aikatan banki yana cewa “ina tsammanin ba ya da lafiya,” yayin da wani ya fara ɗaukar abin ban mamaki.
Vieira Nunes ta ci gaba da cewa ‘Kawun nata’ yana da lafiya, ya kasance mai yin shiru ne, amma ta wannan matakin, ma’aikatan banki sun riga sun kira jami’an gaggawa da ’yan sanda.
“Kawu wani abu kake ji? Bai ce komai ba, haka dai yake,” in ji matar.
Ta ƙara da cewa “Idan ba ka da lafiya, zan kai ka asibiti. Kana so ka sake zuwa ɗakin ba da agajin gaggawa?”
Paulo Roberto Braga bai amsa tambayoyinta ba, kamar yadda ma’aikatan lafiya suka tabbatar da cewa ya mutu aƙalla ’yan sa’o’i.
An kama Vieira Nunes kuma an tuhume ta da laifin tozarta gawa da yunƙurin zamba.
Lauyan Erika de Souza Vieira Nunes ya shaida wa manema labarai a Brazil cewa majiyoyin ’yan sanda sun sauya gaskiyar lamarin.
Ya yi iƙirarin cewa Paulo Roberto Braga yana raye lokacin da Erika ta kai shi bankin, kuma ya mutu ne a lokacin da ake shirin amincewa da lamunin, wanda shaidu za su tabbatar da shi.
A daya ɓangaren kuma ’yan sanda su ne matar ta san cewa ya mutu ne lokacin da ta kawo shi bankin, kuma tana son ta damfari hukumar ce kawai.
A bayyane yake, ita ma ba ’yar uwarsa ba ce, amma dangi ne na nesa. A halin yanzu babu tabbas ko ita ce mai kula da shi.