Ta kai karar mijinta kan tilasta ta yin Sallah a lokacin al’ada
Wata matar aure a garin Gwagwa da ke Abuja ta kai mijinta kotu kan zargin tilasta mata kwanciyar aure da kuma yin Sallah a lokacin da take jinin al’ada. Matar wadda Allah Ya albarkace su da ’ya daya a aurensu mai shekara 3, ta bukaci Kotun Lardi na Birnin Tarayya da ke garin Jiwa Abuja […]
Wata matar aure a garin Gwagwa da ke Abuja ta kai mijinta kotu kan zargin tilasta mata kwanciyar aure da kuma yin Sallah a lokacin da take jinin al’ada. Matar wadda Allah Ya albarkace su da ’ya daya a aurensu mai shekara 3, ta bukaci Kotun Lardi na Birnin Tarayya da ke garin Jiwa Abuja ta raba aurensu.
Alkalin Kotun Mai shari’a Muhammad B. Marafa ya nemi sanin hujjar wanda ake karar kan dalilinsa na tursasa wa matarsa kamar yadda ta yi zargi bayan ya ankarar da shi cewa hakan ya saba da karantarwar Alkur’ani Mai girma da kuma koyarwar Manzon Allah (SAW).
Da yake bayani, wanda ake zargin mai suna Khalid Idris ya musanta zargin kwanciyar aure da matarsa a lokacin da take al’ada, sa dai ya amince a kan ya na tursasa mata ta yi Sallah a lokacin. Ya ce ba ya aiki da Hadisi, sai dai Alkur’ani kadai, inda kuma ya kafa hujjarsa da wata aya da ya karanto.
Sai dai alkalin kotun ya sake ankarar da shi a kan rashin sahihihancin kafa hujja da ayar, sannan ya jawo masa wasu ayoyin. Daga nan ne sai mutumin ya shaida wa kotun cewa akwai yarjejeniya a tsakaninsa da waliyyin matarsa cewa za ta rika yin Sallah ko da tana yin al’ada kafin a daura masu aure da ita.
Kotun ta dage ci gaba zaman don gayyatar waliyin matar da kuma mjinta.