Ta-kai, ta-kai, gobarar bera
Goyon bayan da wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC suka ba Shugaba Muhammadu Buhari don sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasa mai zuwa bai ba kowa mamaki ba, ganin cewa ba su da wata mafita daga halin tsaka mai wuyar da suka jejjefa kawunansu illa hakan. A cikin shekaru biyu da rabin da gwamnonin […]
Goyon bayan da wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC suka ba Shugaba Muhammadu Buhari don sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasa mai zuwa bai ba kowa mamaki ba, ganin cewa ba su da wata mafita daga halin tsaka mai wuyar da suka jejjefa kawunansu illa hakan. A cikin shekaru biyu da rabin da gwamnonin suka yi bisa mulki ba su aikata wani abin-a-zo-a-gani ba don kyautatawa jama’arsu da kuma yi musu jagoranci zuwa inda za su sha romon dimokuradiyya. A siyasance kuma ana iya cewa babu wani abin da suka yi don karfafa jam’iyyarsu ta hanyar hada kan ‘ya’yanta da kawar da kananan rigingimu ko magance yawan gutsuri-tsoma tsakaninsu da talakawansu. Wadannan abubuwan ne suka haddasa matsalolin da suka jefa waigi bisa hanyar tafiyar da ake yi na kaiwa ga canjin da shugabannin jam’iyyar suka alkawarta yayin yakin neman zabe a shekarar 2019.
To, ba za a ce ba a samu canji ba, domin ko a jikin talaka ma ana iya fahimtar gagarumin canjin yanayin da ya wakana a kasar nan. Talaka ya jeme, ya fita cikin kyakkyawan hayyaci sakamakon tsadar rayuwar da rashin aikin yi ya haddasa masa, hakan kuma ya yi sanadiyyar kasawarsa wajen ciyar da iyalinsa da kuma sauke nauyinsu da ke kansa. Masana’antu sun rurrufe saboda rashin kayayyakin ayyukan gudanar da su. Ma’aiktan gwamnati sun fi kowa tagayyara domin dan albashin da ake ba su a karshen wata bai rufa musu asiri, balle kuma magidancin da bai da aikin yi wanda zai agaza masa fita kunyar iyalinsa da yin wasu hidindimu don karan kansa. Haka nan a ke zazzaune a wannan marrar, haihuwar guzuma: da kwance uwa kwance, ba mai tayar da wani.
Gwamnoni na sane da cewa jama’ansu na fama da wahala, amma su ba abin da ya dame su, ba su kuma daukar matakan saukaaka musu radadin wahalhalun da suke fama da su ta hanyar samar da ayyukan yi da inganta asibitoci da makarantu don a daina zuwa na kudi, wadanda talaka ko iyalinsa ba su iya zuwa saboda rashin sa’ida. Abin da kawai gwamnoni suka sa a gaba shi ne kudaden da akan aiko musu da su wata-wata a matsayin kasonsu na arzikin kasa, wadanda talaka bai amfana daga gare su, amma ana cewa ana ware daruruwan miliyoyin Naira daga ciki don inganta sha’anin tsaro kowane wata, sauran da suka rage kuma hatta albashin ma’aikata ba a iya biya, ko kuma idan ma har an turza wajen biyan, to ba za a ba su yadda ya kamata ba sai an yi musu kwange.
Duk da cewa an san ana fama da halin matsi sakamakon tabarbarewar tattalin arziki, amma ai wannan ba dalili ne ba da zai sa gwamnatocin jihohi su shantake, su bar jama’a na tagayyara, alhali kuwa su da iyalansu ba su fama da matsi, da sun ji gari ya fara yi musu tukkar-hagu sai su garzaya wajen Baba Buhari, Shugaban kasa, don ya agaza musu da abin da za su tallafi jama’arsu, amma su ba su taimakawa kamar yadda su aka kyautata musu. Abin takaici game da haka shi ne har yanzu babu wata jiha guda daya da ta kokarta wajen bullo da dabarun magance kanfar kudin da take fama da shi ba tare da dogaro bisa gwamnatin tarayya ba. Watau ke nan idan babu gwamnatin tarayya, ko kuma idan tattalin arzikin kasa ya shiga wata matsala shi ke nan haka nan jihohin za su durkushe, alhali kuwa ga arziki da dimbin albarkatu nan jibge a karkashin kasar da suke bisanta? Babban abin takaici, ko kuma haushi ko abin dariya game da irin wannan harkar shi ne sai ka ga gwamnonin da suka jahilci ainihin halin tattalin arzikin da jiharsu ke ciki sun fi kowa hankoron yin alkawarura marasa kan gado, wadanda ba su da tushe balle wata makama don yaudarar jama’a.
Amma cikin dan lokaci kankane sai gwamnonin suka shantake, da yawa daga cikinsu, musamman ma na yankin Arewa, suka shiga sharholiya da bidiri da dukiyar talakawa, suka mance da ayyukan da ke gabansu har ta kai sun buwayi kowa, ba wanda ya isa ya nemi karin bayani daga gare su game da wani aikin da waninsu ya ce yana yi, ko kuma umurnin da yake bayarwa. Abin da ya fi damunsu kawai shi ne yadda za su farke kudaden da suka karkashe wajen zaben da ya kai su bisa kujerun mulki. Daga nan za su nemi zama dagutu, ba kuma mai ja da su, domin sun zama dodon da kowa ke tsoro, yana kuma yi masa bauta. A lokacin ne za su dauki wani girman kai da fadin rai su dora wa kawunansa, su rika jin cewa sun rika, har suna iya kashewa da rayawa, inda duk suka je, sai ka ji suna yi wa kansu kirari, suna cewa ‘ina wasu ba sui ba?’
Ta haka ne su da talakawa suka raba gari domin sun fahimci cewa mayaudara ne, wadanda ba su kishinsu sai dai kawai abin da za su iya yayyaga daga dukiyar baitulmali don kashewa a yakin neman zabe mai zuwa saboda tsananin kulafucin tabbata bisa mulki. Al’amuran wadannan gwamnonin ba su da tasiri ga talakawan da suka dade da dawowa daga rakiyar su, haka nan kuma talakawa na ganin wallensu saboda rashin damuwa da halin da suke ciki. Gwamnonin sun dade da sanin cewa talakawa sun gano su, sun kuma san cewa makudan kudin da suke samu daga arzikin kasa da kuma wadanda suke tattarawa a cikin gida ba su amfana daga gare su, saboda haka nan jira kawai suke ranar zabe ya zagayo su huce haushinsu a kansu da katunan kuri’unsu
Shi ya sa suke so yadda duk za a kada ko a raya sai sun tabbatar Shugaba Buhari ya sake tsayawa zabe a shekarar 2019, domin su bi Yarima su sha kida, kamar yadda aka yi a shekarar 2015 sa’ilin da ‘Guguwar Buhari’ ta yayo su ta yayyaba bisa mulkin jihohinsu. To a karo mai zuwa talakawa sun ce ta-kai-ta-kai gobarar bera za a yi, kowa tasa ta fisshe shi, ganin cewa a ranar ba wani mai ceton wani sai dai sakayyar talakawa na kyawawan ayyukan da kowane dan takara ya yi wa jama’arsa da kuma irin kyautatawar da ya yi masu.