Ta kama mijinta yana wa ’yar shekara 10 fyade a gadonta
’Yan sanda a Karamar Hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa sun kama wani mahauci da ake zargi da yin lalata da wata yarinya ’yar shekara 10 a dakin matarsa bayan matar ta tafi unguwa. Mahaucin mai suna Magaji Muhammed, mai kimanin shekara 53 dubunsa ta cika ne bayan da matarsa ta yi masa ihu lokacin […]

’Yan sanda a Karamar Hukumar Ringim da ke Jihar Jigawa sun kama wani mahauci da ake zargi da yin lalata da wata yarinya ’yar shekara 10 a dakin matarsa bayan matar ta tafi unguwa.
Mahaucin mai suna Magaji Muhammed, mai kimanin shekara 53 dubunsa ta cika ne bayan da matarsa ta yi masa ihu lokacin da ta kama shi yana yin fyade ga yarinya (an sakaye sunanta) a kan gadonta.
Hakan ne ya sa mahaifin yarinyar Husaini Udu ya sanar da ’yan sandan Karamar Hukumar Ringim halin da ’yarsa take ciki, inda ya ce mahaucin ya yaudari yarinyar ce ta amince ta bi shi zuwa gidansa inda ya sa ta a dakin matarsa saboda yana da tabbacin matar ba za ta dawo da wuri ba ya fara yi mata fyade. Ya ce yana fara yi wa yarinyar fyade ke nan sai matar tasa ta dawo ta kama shi da yarinyar a kan gadonta.
Da yake amsa tambayoyin ’yan sanda Magaji Mainama, ya ce ya aikata laifin yin lalata da karamar yarinya a dakin matarsa. Kuma ya ce ya dauki lamarin a matsayin tsautsayi ko kuma sa hannu ne na abokan sana’a, ya sa ya fada cikin wannan mugun aiki domin bai taba tunanin aikata haka ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da labarin, inda ya ce mahaifin yarinyar ne ya kai kuka ofishinsu na Ringim ya sanar da ’yan sanda halin da ’yarsa take ciki kuma shi ne ya yi karar Magaji yana bukatar a bi masa hakkin ’yarsa.
Ya ce bayan kama wanda ake zargin sun mika shi ga sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar da ke Dutse domin fadada bincike, kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da shi a a gaban kotu.
A wani labarin kuma wani tsoho mai shekara 55 mai suna Malam Ibrahin Husaini da ke zaune a Unguwar Kofar Kotu a garin Guri a Karamar Hukumar Guri, a Jihar Jigawa ya shiga hannu hukuma bisa zarginsa da yin fyade ga wata yarinya ’yar shekara 8 (an sakaye sunanta).
’Yan sanda sun kama wanda ake zargin tare da gabatar da shi a gaban Kotun Majistare da ke Dutse, inda wanda ake zargin ya musanta laifin da ake tuhumarsa, ya ce sharri aka yi masa domin a bata masa suna, kuma ya nemi ta ba da belinsa.
Alkalin Kotun Mai shari’a Usman Muhammed Lamin ya ingiza keyar wanda ake tuhumar zuwa kurkukun da ke Garu a Karamar Hukumar Dutse zuwa ranar 3/8/2017 domin ci gaba da shari’arsa,bisa dogaro da sahi na 282 na kundin laifuffuka na Jihar Jigawa.