… Ta Kano ta tube kanen Gwamna Ganduje daga dagaci

A ranar Litinin din da ta gabata ne Majalisar Masarautar Kano ta bayar da sanarwar tube kanen Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wato Alhaji Sani Umar Ganduje daga sarautarsa  ta Dagacin Ganduje da ke jihar.Bayanai sun ce kimanin wata biyu da suka gabata ne Masarautar Kano ta dakatar da Alhaji Sani Ganduje daga […]

… Ta Kano ta tube kanen Gwamna Ganduje daga dagaci
… Ta Kano ta tube kanen Gwamna Ganduje daga dagaci

A ranar Litinin din da ta gabata ne Majalisar Masarautar Kano ta bayar da sanarwar tube kanen Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje wato Alhaji Sani Umar Ganduje daga sarautarsa  ta Dagacin Ganduje da ke jihar.
Bayanai sun ce kimanin wata biyu da suka gabata ne Masarautar Kano ta dakatar da Alhaji Sani Ganduje daga sarautar Dagacin bisa zarginsa da cin kudin maniyyata aikin Hajji a yankinsa, inda masarautar ta kafa wani kwamiti domin ya gudanar da bincike akan lamarin.
Aminiya ta samu bayanin cewa masarautar ta dauki matakin warware rawanin Dagacin ne bayan da kwamitin ya same shi da hannu dumu-dumu a cikin harkalla cin kudin maniyyata aikin Hajjin da suka fito daga garin Ganduje a yankin kramar Hukumar Dawakin Tofa da ke jihar.
Har ila yau masarautar ta ce baya ga cinye kudin maniyyatan, kwamitin ya gano yadda Dagacin yake cin zarafin jama’arsa ta hanyar nuna musu gadara da karfin mulki. Kuma an gano Dagacin yana yawon maula a ofisoshin gwamnati daban-daban.
A cikin sanarwar tube Dagacin, an ruwaito Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II yana kira ga dagatai da sauran masu rike da shugabacin al’umma a jihar a koyaushe su zama masu tsoron Allah wajen yin hulda da mabiyansu.