Ta karya ’yar riko saboda ta yi mata kashi

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata matar aure mai suna Rabi Salihu bisa zargin ta da karya kafar ’yar rikon da aka kai mata saboda yi mata kashi a kan kujera.Wadansu mata ne da suke zaune gida guda da matar a Unguwar kofar Waika suka sanar da Hukumar Hisba cewa Rabi Salihu ta […]

Ta karya ’yar riko saboda ta yi mata kashi
Ta karya ’yar riko saboda ta yi mata kashi

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wata matar aure mai suna Rabi Salihu bisa zargin ta da karya kafar ’yar rikon da aka kai mata saboda yi mata kashi a kan kujera.
Wadansu mata ne da suke zaune gida guda da matar a Unguwar kofar Waika suka sanar da Hukumar Hisba cewa Rabi Salihu ta dauki yarinyar da take riko mai suna Nana Badiha Ishak mai kimanin shekara uku da haihuwa ta yi jifa da ita a jikin bango, sannan ta rika tattaka ta lamarin da ya yi sanadiyyar karyewarta.
Sai a nata bangaren Rabi ta musanta laifin da ake zargin ta da shi, inda ta bayyana gaba dayan lamarin a matsayin tsautsayi. “Wannan abu tsautsayi ne domin lokacin da ta yi min kashi a kan kujera na yi mata fada. Sannan na dauko ta daga daki inda na umarce ta ta tafi ban-daki in wanke mata jikinta, to saboda na yi amfani da sabulu na ajiye shi a wurin, sai tsantsin sabulu ya kwashi yarinyar ta fadi ta karye. Amma karya ne da ake cewa na yi jifa da ita har ta karye. Ta yaya hakan za ta faru? ’Yar yayana ce fa aka ba ni rikonta, saboda ba ni da dan kaina. Na haihu da yawa amma duk ’ya’yan sun rasu,” inji ta.
A cewarta a yanzu haka ma tana addu’a Allah Ya ba yarinyar lafiya ta ci gaba da rikon ’yarta. “Yanzu ma ina addu’ar Allah Ya ba ta lafiya in ci gaba da rikon abata. Allah Ya raya min ita,” inji ta.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar Hukumar Dala, Malam Abubakar Mati Salihu ya shaida wa Aminiya cewa wannan ba shi ne karo na farko da matar ta aikata irin wannan laifi ba, domin a kwanakin baya sai da hukumar ta shiga tsakani a lokacin da aka same ta da laifin azabtar da ’yar mijinta wacce daga baya aka mayar da ita hannun mahaifiyarta.
Mataimakin Kwamandan ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta gurfanar da matar a gaban shari’a don yi mata hukunci.