Ta kashe dan kishiyarta a kan Naira 200

A makon da ya gabata ne wata mata mai suna Nana Shamsiyya da ke zaune a Unguwar Sarki, garin Guibi da ke karamar Hukumar Kudan, Jihar Kaduna aka yi zargin ta kashe dan kishiyarta saboda kudin cefane, Naira dari biyu.A binciken wakilinmu, ya gano cewa, wani bawan Allah ne mai suna Saleh mai rake, wanda […]

Ta kashe dan kishiyarta a kan Naira 200
Ta kashe dan kishiyarta a kan Naira 200

A makon da ya gabata ne wata mata mai suna Nana Shamsiyya da ke zaune a Unguwar Sarki, garin Guibi da ke karamar Hukumar Kudan, Jihar Kaduna aka yi zargin ta kashe dan kishiyarta saboda kudin cefane, Naira dari biyu.
A binciken wakilinmu, ya gano cewa, wani bawan Allah ne mai suna Saleh mai rake, wanda ke zaune a garin ya wayi gari da tashin hankali tsakanin matansa biyu, uwargida da amarya, dukkansu suna zaune ne a gida daya. Uwargidan sunanta Shamsiyya, amaryar kuma Nana Aishatu.
Wannan tashin hankalin ya biyo bayan tambayar da uwargidan tasa ta yi masa a kan ya ba ta kudin cefane, inda nan take ya dauko Naira 200 ya ba ta, ya kama hanya zai fita ke nan sai amaryar tasa ita ma ta ce tana bukatar nata kudin cefanen. Nan take sai ya kawo Naira dari 200 ya ba ta. Sai ta ta ce ba zai ishe ta ba, domin ga yaro nan ba shi da lafiya, za ta saya masa magani.
Hakan ya sa uwargidan ta fusata, shi kuma ya kama hanya ya fita. Bai dade da fita ba matan nasa suka kaure da fada. Bayan an raba su sai aka ce amaryar ta fita waje ta bar uwargidan a cikin gida. Ganin haka sai ita uwargidan ta je dakin amaryar, inda yaronta ke barci. Aka ce ta dauko yaron ta buga shi da kasa, inda nan take ya mutu.
Wakilin Aminiya ya tuntubi DPO mai kula da shiyyar Kudan Buhari T. batagarawa don tabbatar da labarin, inda ya ce tabbas yaron ya mutu amma dai shi an ce masa yaron ya fado ne daga bayan mahaifiyarsa, a lokacin da suke dambe, wanda hakan ya sa ya mutu kai tsaye. Ya kara da cewa, ya bayar da umurnin a kai su babban ofishinsu na Zariya don ci gaba da bincike.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin ’yan sanda na shiyyar Zariya don jin inda aka kwana amma jami’an da suke binciken lamarin sun ce ba za su iya cewa komai ba, domin ba su kammala bincike ba.