Ta kashe dan mijinta saboda ya fasa mata madubi
Bayan ya fasa mata madubi, sai ta je ta dauko wuka ta luma masa a wuya, sheka lahira
Wata matar aure ta daba wa dan mijinta wuka tare da aika shi lahira saboda ya fasa mata madubi.
Matar ta luma wa matashin mai shekara 18 wuka a wuya, ya ce ga garinku nan ne a sakamakon sa-in-sa da suka samu a tsakaninta da matsahin, wanda da ne ga dan uwan mijinta, har ta kai ga matashin ya fasa madubin da ke gidan.
Ita kuma nan take ta zarce zuwa dakin girki da dauko wukar girki, wanda ba ta bata lokaci ba, ta caka masa wukar a wuya, ya ce ga garinku nan.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce ’yan sanda daga Babban Ofisin ’Yan Sanda na yankin Agbado sun damko matar mai shekara 30 a ranar Asabar, bayan sun samu kiran neman dauki game da bin da ya faru.
Kakakin Rundunar ya shaida wa manema labarai cewa jami’an da suka je wurin sun iske matashin kwance a cikin jini, suka dauke shi zuwa asibiti, inda likitoci suka tabbatar da ya rasu.
Ya ce ita kuma matar ana tsare da ita a hannun Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunan, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole.