Ta kashe jaririn da ta haifa a bandaki

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda Jihar Legas da ke unguwar Yaba yana binciken wata matashiya mai suna Farida ’yar shekaru 22 kan zargin kisan jaririn da ta haifa a wani bandakin gidan wanka da ke kasuwar Alaba Rago ta jihar.Asirin Farida, ’yar asalin kasar Togo ya tonu ne a karshen makon da […]

Ta kashe jaririn da ta haifa a bandaki

Sashen binciken manyan laifuka na rundunar ’yan sanda Jihar Legas da ke unguwar Yaba yana binciken wata matashiya mai suna Farida ’yar shekaru 22 kan zargin kisan jaririn da ta haifa a wani bandakin gidan wanka da ke kasuwar Alaba Rago ta jihar.
Asirin Farida, ’yar asalin kasar Togo ya tonu ne a karshen makon da ya gabata yayin da ta cusa yaron a shaddar tangaran ta wani gidan wanka jim kadan da haihuwarsa inda hakan ya yi sanadin mutuwarsa.
Wani mai suna Malam Shu’aibu, wanda ya gane wa idonsa lamarin, ya bayyana cewa, “Yarinyar ta haife jaririn a wani gidan wanka da ke cikin kasuwarmu, sai ta cusa shi da karfi a cikin masai, to da ma masan na zamani ne na tangaran sai yaron bai tafi cikin masan gaba daya ba, ita kuma ta yi zaton yaron ya bi ruwa ya fada shadda. Da wata mata ta shiga ban dakin sai ta ga jini kaca-kaca a ciki, da ta duba sai ta ga jariri a ciki. Nan da nan ta sanar da masu gidan wankan aka kama yarinyar. Muna zaton tuni ta kashe yaron ba a sani ba, amma kuma alamu sun nuna cewa a cikin bandakin ta haife shi, don ga alamun jinin haihuwa nan a ko’ina da kuma jikinta”.
Ya bayyana cewa tambayoyin da shugabannin kasuwa suka yi mata sun nuna cewa ba ta san wanda ya yi mata cikin ba kuma shi ne ciki na farko da ta taba yi.
Masu gidan wankan sun bayyana cewa ba su ji  kukan jariri ba a lokacin da Farida ta shiga bandakin, har sai da wata ta shiga sannan ta sanar da su halin da ake ciki.
Wata mai suna Rafa, wacce ake zargi da ita ce uwargijiyar Farida, ta musanta cewa  ita ta kawo ta kasuwar.
Rundunar ’yan sanda ta bayyana cewa da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da Farida gaban alkali.