Ta kashe jaririyarta, ta jefa gawar a kogi
Jami’an ’yan sanda sun cafke wata mata mai bisa zargin kashe jaririyarta ’yar wata daya tare da jefa gawarta a cikin kogi. Dubun matar mai shekara 35 ya cika ne bayan ’yan sanda da ke sintiri daga caji ofis din Enugada sun titsiye ta bayan sun yi sun yi tantama da suka ga tana jefa […]
Jami’an ’yan sanda sun cafke wata mata mai bisa zargin kashe jaririyarta ’yar wata daya tare da jefa gawarta a cikin kogi.
Dubun matar mai shekara 35 ya cika ne bayan ’yan sanda da ke sintiri daga caji ofis din Enugada sun titsiye ta bayan sun yi sun yi tantama da suka ga tana jefa wani abu a cikin kogi.
- ‘Yadda na gudu a hannun masu garkuwar da suka kama mu’
- Okorocha ya ci bugu a hannun basarake
- Guguwa ce ta sa na ‘samu juna biyu’ —Mace
Kakakin ’yan sanda a Jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce, da ’yan sandan suka ji ba su natsu ba, nan take suka damke ta suka shiga yi mata tambayoyi.
Oyeyemi ya ce, “A wurin binciken ne ta bayyana cewa gawar jaririyar da ta haifa wata daya da ya wuce ne ta jefar, kuma tsananin damuwa ya sa ta kashe jaririyar.
“Ta ce wanda ya yi mata cikin ne ya ki karbar ’yarsa, ita kuma da ta ga ba ta halin kula da ita, sai ta kashe ta, ta jefar a kogi,” inji Oyeyemi.
Ya ce a yayin binciken an garo “kafin ta haifi jaririyar, matar ta haifa wa wasu maza uku ’ya’ya shida, amma mahaifin jaririyar da aka kashe ya ki karbar ’yarsa.”
Oyeyemi ya ce daga baya masu ninkaya sun ciro gawar jaririyar aka kai ta dakin ajiyar gawa a Babban Asibiti.
Ana kan bincike game da abin da ya faru kafin a gurfanar da wadda ake zarign a gaban kotu.