Ta kashe kanen mijinta don yin ramuwar gayya
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mace bisa zarginta da kashe wani yaro kanen tsohon mijinta don yin ramuwar gayya a kan mahaifiyarsa. Matar mai suna Nusaiba wacce shekarunta ba su wuce 15 ba, ana zargin ta aikata laifin ne ta hanyar sace yaron mai kimanin shekara 10 tare da jefa shi a […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wata mace bisa zarginta da kashe wani yaro kanen tsohon mijinta don yin ramuwar gayya a kan mahaifiyarsa.
Matar mai suna Nusaiba wacce shekarunta ba su wuce 15 ba, ana zargin ta aikata laifin ne ta hanyar sace yaron mai kimanin shekara 10 tare da jefa shi a cikin rijiya ya mutu.
Aminiya ta ji cewa an dade ana kai ruwa rana tsakanin Nusaiba da mahaifiyar mijin Nusaiba mai suna Amina, lamarin da ya jawo rabuwar aurensu.
Mahaifiyar yaron mai suna Amina ta shaida wa Aminiya cewa bayan ta dauki awanni ba ta ga danta ba sai ta shiga nemansa a nan ne wasu mutanen unguwar suka shaida mata cewa an gan shi tare da wata mace wacce ta lullube fuskarta da nikabi. “Tunda
mutanen suka gaya min cewa an ga dana da wata mai nikabi ba mu sake jin duriyarsa ba sai bayan kwana biyu aka tsinci gawarsa ta fara lalacewa. Bayan kwana biyu da tsintar gawar dana sai (tsohuwar surkata) ta bugo waya ta ce “tunda kika raba ni da mijina, shi ya sa na yi alkawarin sai ni ma na raba ki da naki dan.”
Wacce ake zargin ta amsa laifinta a gaban ’yan sanda inda ta ce aikin shaidan ne.
Kakakin ’yan sandan Kano ASP Magaji Musa Majiya ya cewa rundunarsu ta tura wadda ake zargin zuwa kotu don yi mata shari’a. “Lura da shekarunta ba su wuce 15 ba, ba
za mu iya kai ta kowace kotu ba, saboda haka muka rubuta takarda ga ma’aikatar shari’a don samun shawara kan abin da ya fi dacewa,” inji shi.