Ta kashe kanta saboda mijinta zai kara aure

Bayan sun samu sabani da shi ta je ta sayo guba ta kwankwadi abinta.

Ta kashe kanta saboda mijinta zai kara aure

Gawa

Wata mata aure ta kashe kanta ta hanyar shan guba saboda mijinta zai yi mata kishiya.

Matar wadda suke da ’ya’ya biyu tare da mijin nata ta kwankwadi gubar ce bayan sun samu sabani da shi kan shirinsa na kara aure, saboda Musulunci bai hana ba.

Wani dan uwan mijin marigayiyar mai suna Alhaji Lagbe Araoje, ya ce, “Ranar Litinin da misalin karfe 10 na safe ta samu sabani da mijinta a waje, amma aka sasanta su. Daga baya mijin nata ya ba ta wata waya da take so.

“Bayan ’yan mintoci sai aka gan shi ya fito daga gidan yana kuka cewa matarsa tana amai.

“A hanyarmu ta kai ta asibiti ta rika rokon shi ya yafe mata, tana bayyana cewa wani garin hoda da ake kira DDT ko Sniper ta sha.

“Daga baya Allah Ya yi mata cikawa a asibiti da misalin karfe 12 na rana,” a Babban Asibitin Ilori da ke Jihar Kwara.

Wani mai kemis a yankin da abin ya faru ya tabbatar cewa marigayiyar ta sayi Sniper a kantinsa.

Amma wata wadda ta ce abokiyar karatun mamaciyar ce, ta yi zargin cewa surukar mai rasuwar ce ta sanya mata guba, saboda sun samu sabani kan addinin da marigayiyar wadda Kirista ce.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina