Ta kashe Naira miliyan 5 a liyafar bikin auren kanta da kanta
Danni ta ce ba za ta nemi gafara ba saboda son da take yi wa kanta ko na bikin aurenta.
Wata matar da ta yi suna a wajen gyaran jiki mai suna Danni ta ce ba za ta nemi gafara ba saboda son da take yi wa kanta ko nuna bikin aurenta – inda ta sha alwashin yin haka a kafafen yaɗa labarai.
Danni mace ce mai ƙarfin hali da ta ce ba ta neman gafarar kowa a kan buƙatarta don haka ta kashe kuɗaɗe wajen shagalin bikin auren kanta da kanta.
- Mai shafe minti 6 yana fesar da ruwa daga baki
- Majalisar Kaduna ta buƙaci bayanan kashe kuɗaɗe a mulkin El-Rufa’i
Danni tana koyar da gyaran jiki a hoto kuma ta yi tasiri a gyaran jikin, kuma tana zaune a birnin Los Angeles a Jihar Kalifoniya da ke Amurka.
Ta yi bikin aure na gargajiya ta hanyoyi da yawa, ta gayyaci dangi da ƙawayenta, inda ta yi liyafar ba da kyautar furanni da karanta alwashin yin bikin auren kanta – amma, lokacin da ta kai ga ƙarshen bayanin bikin ta kalli wani babban madubi, tana cewa “A shirye nake in ɗaura aura aurena ga kaina.”
Danni ta ce ta yi ‘mafarkin’ ta auri kanta tun tana ƙarama, ba ta taɓa fahimtar ra’ayin wani mutum ya sauya mata tunani ba kuma ta bayyana a kafar YouTube’s cewa, “Ba a yin hukunci kan soyayya, bikin aure game da amarya ne.”
Haifaffiyar Florida ta kashe Dala 4,000 (kimanin Naira miliyan 5 da dubu 278 da 400 a bikin aurar da kanta ga kanta. Ta ce ita ba ’yar iska ba ce, amma Danni wacce ta auri kanta da kanta tana da “ƙwarin gwiwa kawai,” duk da tunanin mutane.
Danni ta ce, kafin ɓarkewar cutar COVID-19 a shekarar 2020, ta so ta auri kanta da yin bikin auren – amma bayan tsaka-mai-wuya sai ta ga yana da ma’ana mai zurfi – soyayyar kai.
Ta faɗa cikin kogin soyayyar kanta, kuma ta yanke shawara don inganta rayuwarta daga barin shaye-shaye zuwa neman magani.
Danni ta ce: “Na shafe lokaci mai kyau tare da kaina, na ɗauki ranar auren kaina. Kawai don gano abin da nake so.
“Na zo da shawarar in auri kaina kafin cutar COVID amma ba a yi bikinta ba har zuwa 2022.”
Ta ƙara da cewa: “Bikin ɗaura aurena shi ne zai sa in bayyana abubuwan da suka hana ni son kaina.
“Ba na cutar da kowa. Lokacin da na isa harabar ɗaura aurena na kasance mai matuƙar damuwa.”
Amarya ta isa harabar tare da ’yan uwanta da wani madubi da aka ajiye gefe wanda take kallonsa a lokacin da take faɗin kalmomin ɗaura auren, sannan ta sumbaci bakinta a jikin hotonta na madubin.
’Yan uwa da abokan arziki masu goyon bayanta sun yi murnar bikin tare da ita.
Duk da haka, bikin nata da ba a saba gani ba ya fuskanci suka da yawa bayan da ta fito fili ta yaɗa shi ta shafukan Intanet kuma ta yi magana a talabijin.
Wani mai sharhi ya ce: “Wannan shi ne mafi soyayyar kai da mutum bai son wani ya kusance shi da na taɓa gani!”
Danni ta ce: “Maganar da ta fi ɓata min rai a shafukan Intanet ita ce mutane na cewa na auri kaina domin babu wanda zai so ni.
Ta ce “Wane saƙo ne muke tura wa jama’a wanda ba a son su, da ba su cancanta ba? Wannan ba gaskiya ba ne, gobe zan iya auren namiji!”
Amma Danni ta zaɓi ta mai da hankali a kan kanta da kuma ƙwarin gwiwar da za ta iya bai wa wasu.
Danni, wacce ta bayyana kanta a matsayin “Yarinya mai zamani” ta yarda cewa kasancewa cikin soyayya da wani ya sha bamban da kasancewa cikin soyayyar kanka da kanka.
“An samu ranar aure da kwanan wata a baya, amma babu ɗaya daga cikin mutanen da suka cika wannan alƙawarin,” in ji ta.
Tana fata ta yi auren soyayya wata rana kuma za ta iya kasancewa a cikin ranar yin aure.
A yanzu dai babban burinta shi ne ta zaburar da wasu su so kansu.
“Ina son kaina kuma ba zan nemi afuwar haka ba. Zan ci gaba da ƙarfafa wa mata gwiwa da kuma nuna wa ƙananan ’yan mata cewa son kansu shi ne mafi kyawun abin da za su iya yi,” in ji ta.