Ta kashe ’yarta kan naira 40
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato tana neman wata mata mai suna A’isha Abubakar bisa zarginta da kashe ‘yarta ‘yar shekara 13 mai suna Balki Abubakar, don ta zubar da naira 40 da ta aike ta ta sayo mata magi. Wannan al’amari dai ya faru ne a unguwar rogo da ke garin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.Wata […]

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato tana neman wata mata mai suna A’isha Abubakar bisa zarginta da kashe ‘yarta ‘yar shekara 13 mai suna Balki Abubakar, don ta zubar da naira 40 da ta aike ta ta sayo mata magi.
Wannan al’amari dai ya faru ne a unguwar rogo da ke garin Jos fadar gwamnatin jihar Filato.
Wata majiya da ke kusa da gidan da al’amarin ya faru ta bayyana cewa marigayiya Balki wadda take aji shida na makarantar firamare ta gamu da ajalin nata ne bayan da mahaifiyarta A’isha ta aike ta da kudi naira 40 domin ta sayo mata magi a shago, amma sai ta zubar da kudin a hanya.
Majiyar ta ce, jin bayanin cewa marigayiyar ta zubar da kudin da aka aike ta bayan da ta dawo, nan take mahaifiyar ta shigar da ita daki ta kulle ta ta yi ta dukanta har ta mutu.
Majiyar ta ce, da faruwar wannan al’amari sai A’isha ta kwashe sauran yaranta guda uku ta gudu zuwa kauyensu da ke karamar hukumar Riyom a jihar ta Filato.
Wakilinmu ya yi kokarin saduwa da mahaifin yarinyar mai suna Abubakar Adamu amma abin ya ci tura, domin tun lokacin da abin ya faru ya bar garin. Amma wata majiya ta tabbatar wa da wakilinmu cewa Abubakar ya je ofishin ‘yan sanda na unguwar rogo kuma ‘yan sanda sun ce ya je ya kawo wannan mata tasa da ta aikata wannan aika-aika.
Da yake zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, kakan marigayiyar Malam Adamu Mai nama, wanda yake zaune a Unguwar ‘yan shanu da ke garin Jos, ya bayyana cewa, “a gaskiya mun yi matukar bakin ciki da faruwar wannan al’amari.’’
Ya ce, wani karin bakin ciki kan wannan al’amari shi ne, bayan faruwar wannan al’amari wannan mata ta gudu da sauran yaran nata guda uku zuwa karamar hukumar Riyom.
Ya ce bai kamata a ce wannan karamin abu ya yi sanadin a doki yarinyar har a kashe ta ba. “Ba za mu iya zuwa wajen da aka ce ta gudu ba, domin an ce wai ta gudu ne zuwa wajen iyayenta a karamar hukumar Riyom.’’ Ya ce dama a cikin garin Jos ne dan nasa ya aure ta.
Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, wani daga cikin shugabannin al’ummar Unguwar Rogo, Malam Abdullahi Muhammad, ya bayyana takaicinsa kan faruwar wannan al’amari.
Ya ce a lokacin da ya sami labarin faruwar wannan al’amari, nan take ya kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda na Unguwar Rogo, kuma nan take suka ba shi ‘yan sanda guda biyu suka isa gidan da wannan al’amari ya faru inda suka tarar da yarinyar a kwance har ta mutu.
Da take zantawa da wakilinmu kan wannan al’amari, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Felicia Anslem ta tabbatar da mutuwar wannan yarinya. Ta ce amma har yanzu ba su san dalilin mutuwar yarinyar ba kuma ba su samu damar kama kowa kan wannan al’amarin ba.
Ta ce sun samu wannan labari kuma tuni an yi jana’izar wannan yarinya kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Kuma rundunar ‘yan sandan tana iyakar kokarinta wajen ganin ta kamo wannan mata domin a gurfanar da ita a gaban shari’a.
Ta ce, “babbar matsalar da muke fuskanta kan wannan al’amari shi ne rashin hadin kan da muke samu daga wajen mahaifin wannan yarinya, wajen gano inda mahaifiyar wannan yarinya ta boye.