Ta kashe yayarta don ta mallake gidanta

Wata mata mai suna Habiba Amadu [Kasuwa] ta kashe yayarta mai suna Hajiya Hadiza Amadu domin ta mallake gidanta a cikin dare ranar lahadin da ta gabata a kauyen kauran dan Gambo da ke kusa da garin Lere a jihar Kaduna. Ita dai Habiba Amadu [ Kasuwa ] ana zargin ta da kashe yayar tata […]

Ta kashe yayarta don ta mallake gidanta

Wata mata mai suna Habiba Amadu [Kasuwa] ta kashe yayarta mai suna Hajiya Hadiza Amadu domin ta mallake gidanta a cikin dare ranar lahadin da ta gabata a kauyen kauran dan Gambo da ke kusa da garin Lere a jihar Kaduna.

Ita dai Habiba Amadu [ Kasuwa ] ana zargin ta da kashe yayar tata ne tare da taimakon danta mai suna Adamu Haruna da kuma wani abokinsa, inda suka yanka marigayiyar suka saka ta a cikin buhun leda, suka haka rami a bayin cikin gidanta suka binne ta.
Da take yi wa wakilinmu bayani kan yadda al’amari ya faru, matar yaron dan wadda ake zargin, mai suna Fatima Waziri ta ce, “kwanana tara muna tare da marigayiya a gidanta, sai maigidana ya ce in yi tafiya, na ce in yi tafiya a kan me? Ya ce in tafi garinmu in yi kwana biyu in dawo, na ce ba zan je ko’ina ba. Sai ya ce bari ya je wajen mahaifiyarsa a garin Lere ya dawo.’’
Ta ci gaba da cewa, ‘’da ya tafi wajen mahaifiyarsa a Lere ya dawo, sai ya ce mahaifiyarsa ta ce in je. Da yamma ta yi sai na tafi wajen mahaifiyar tasa, muna tare da ita har bayan sallar isha’i, sai ta kama hanya ta taho wannan kauye na kauran dan Gambo. Bayan ta koma cikin dare sai ta tashe ni, ta ce ta fito wajen Hajiya Hadiza ne sun zauna da ita ta sayar mata da gidanta, sai na ce Allah Ya bada sa’a, na koma na kwanta,’’ inji ta.
Ta kara da cewa, ‘da gari ya waye sai mai gidan nawa ya zo ya same ni ya ce ya sayi gidan Hajiya Hadiza kan kudi naira miliyan 1 da dubu 300. Na ce masa a ina ne ya samu kudin da ya sayi gidan? sai ya ce ya je ya sayar da kadarorinsa ne a garin Lafiya. Sai na ce masa ita Hajiya Hadiza fa tana ina? sai ya ce mani ta kwashe kayanta ta yi tafiya.’’
“Da yamma ta yi sai ya tattaramu muka dawo wannan kauye, sai na kara tambayarsa ina Hajiyar ? sai ya ce mani ai ba ta nan ta tattara kayanta ta yi tafiya. Akwai wata wukar da ya fita da ita a aljihunsa, sai na tambaye shi ina za shi da wuka, sai bai ce mani komai ba. Ya sanya ni girkin abinci, da zan yanka albasa sai na nemi wuka na rasa, na tambaye shi ina wuka sai ya ce mani ya barta a waje. Da na shiga bayi sai naga wukar da ya ce ya barta a waje duk jini a jikinta, sai na dauki wukar na ce wannan wukar da ka ce ka barta a waje yaya na ganta a bayi duk da jini a jikinta?’’
Ta ce, ‘’bayan haka muna zaune sai na ga wani sabon simintin da ban taba gani ba a bayan gidan. Sai na tambayi mahaifiyar mai gidan nawa wannan sabon siminta fa? sai ta ce wai ta binne wani abu ne saboda makiya. Ta ce ina ta tambayarsu amma suka ki su ba ni hadin kai, daga nan sai na yi shuru,’’ inji ta.
“Bayan haka sai mahaifiyar mijin nawa ta cigaba da zirga-zirgar wai a sanya mata hannu kan takarda ta sayi gidan marigayiyar. Tana ta bin ‘yan uwanta da kudade a sanya mata hannu.’’
Ta ce, Daga bisani ne aka kai mu wajen Hakimin Lere, daga nan aka tattaramu aka kai mu ofishin ‘yan sanda na garin Saminaka. Da muka je na yi masu bayani, aka zo aka bincika aka gano inda suka binne marigayiyar.
Ita ma da take yi wa wakilinmubayani, wata kanwar wadda ake zargin mai suna Rabi Amadu ta bayyana cewa, ‘’a lokacin da marigayiyar ta gina wannan gida sai ta kira ni ta ce Rabi wannan gida ko da Allah ya karbi raina na bai wa ‘yayanki tun da ni bani da ‘yaya, amma komai nawa ‘yan uwa su raba. Ashe a lokacin ita wannan yaya tamu da ta aikata wannan abu abin ya yi mata zafi. A lokacin da yaron ta ya yi aure sai ta ta roki marigayiyar ta bai wa yaron nata aron daki a gidan don su zauna da matar da ya aura. Bayan an kawo amarya da kwanaki tara, sai suka taru da dan nata da wani abokinsa suka kashe ta. Kuma ta fito ta ce wai ta sayi gidan daga wajen marigayiyar kan kudi naira miliyan 1 da rabi. Mun kira duk inda ya kamata mu kira amma ba mu samu labarin inda marigayiya ta shiga ba.’’

 

 

 

 

 

 

 

“Sai na ce da Habiba, Hajiya fa ba ta abu da ka, duk inda za ta tafi sai ta fada mana. Kuma duk abin da za ta yi sai ta yi shawara, don haka babu yadda za a yi ta daga gida ta sayar ba tare da ta shawarce mu ba. Na ce mata ni ban amince ta sayar maki da gida ba, sai kin nemo mana ita duk inda kika kai ta.’’
Rabi ta ce, ‘’daga nan muka kai ta wajen Sarkin unguwarmu, ya dauke mu ya kai mu wajen Hakimi. Hakimi ya yi iyakar yinsa don ta fadi gaskiyar yadda aka yi ta ki ta fada. Daga nan Hakimi ya hada mu da ‘yan sanda aka dauke ta aka tafi da ita garin Saminaka aka hada mu da DPO, ya yi mata tambaya amma ba ta gaya masa gaskiya ba. Da matar danta ta yi bayani, ta ce ta ga wuka kuma ta ga sabon siminti a gidan amma ba ta san abin da yake faruwa ba, saboda lokacin da za su aikata wannan abu sun kore ta daga gidan. Sai aka dauko ta a motar ‘yan sanda aka kawo ta gidan aka ba ta diga ta nuna wajen da suka binne ta, ta hako wajen da kanta. Ana dubawa sai ga gawarta sun yanka ta sun fasa mata kai suka sanya ta a buhun leda suka daure suka sanya a cikin ramin suka rufe.’’
Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, Wazirin Lere kuma Hakimin gundumar Birni da kewaye na masarautar Lere, Alhaji Umaru Muhammad, ya bayyana takaicinsa kan faruwar wannan al’amari. Ya ce ‘’a gaskiya wannan al’amari ya ba mu tsoro kwarai da gaske, domin ba mu taba ganin wani abu mai kama da wannan ba a wannan yanki.’’
Ya ce, “ya kamata mutane su gane cewa duk abin da mutum ya aikata ya sani cewa idan ya je lahira za a tambaye shi.’’
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar ya tabbatar da faruwar wannan al’amari. Ya ce tuni sun riga sun kama wannan mata da ake zargi tare da abokin yaron nata, amma suna nan suna neman yaronta don cigaba da bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu.