… Ta koro ‘yan Najeriya dubu 12

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce ‘yan kasar kusan su 12,000 sun fara isowa gida daga iyakar jamhuriyar Kamaru bayan da aka ba su umarnin su bar kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.NEMA ta ce mutanen sun soma isa kauyen Sahuda da ke […]

… Ta koro ‘yan Najeriya dubu 12
… Ta koro ‘yan Najeriya dubu 12

A shekaranjiya Laraba ne Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta ce ‘yan kasar kusan su 12,000 sun fara isowa gida daga iyakar jamhuriyar Kamaru bayan da aka ba su umarnin su bar kasar, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.
NEMA ta ce mutanen sun soma isa kauyen Sahuda da ke garin Mubi a Jihar Adamawa.
‘Yan gudun hijira – wadanda  akasarinsu ‘yan Jihar Barno ne – wadanda  suka gudu daga hare-haren da ‘yan Boko Haram suke kai wa yankunansu, na samun mafaka ne a kasar Kamaru.
Sai da jami’an shiga da fice na Najeriya da jamian tsaro suka binciki mutanen da suka dawo gida. Hukumar NEMA ta ce kawo yanzu karbi ‘yan gudun hijira 1,121 daga jami’an shiga da fice na Najeriya a iyakar, inda ta tura 650 daga cikinsu zuwa jihar Barno, yayin da ragowar har yanzu na sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Yola.