Ta majalisa ne kawai za a cimma nasarar sake fasalin Najeriya-Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya ce ta hannun majalisar tarayya ne kawai za a iya cimma burin rajin sake fasalin kasar. Shugaban Majalisar ya yi furucin ne jiya a Abuja yayin da yake jawabin maraba ga ’yan majalisar saboda dawowa hutun shekara da suka yi lafiya. Ya bayyana cewa majalisar za ta sake bibiyar […]

Ta majalisa ne kawai za a cimma nasarar sake fasalin Najeriya-Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ya ce ta hannun majalisar tarayya ne kawai za a iya cimma burin rajin sake fasalin kasar.
Shugaban Majalisar ya yi furucin ne jiya a Abuja yayin da yake jawabin maraba ga ’yan majalisar saboda dawowa hutun shekara da suka yi lafiya.
Ya bayyana cewa majalisar za ta sake bibiyar gyaran fuskar da ake yi wa kundin tsarin mulkin kasar don sanya lamuran sake fasalin kasar ciki.
Amma idan ba a manta ba majalisar ta yi fatali da batun sake fasalin kasar da ya shafi raba iko tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi yayin da ’yan majalisar suka kada kuri’a kan gyaran fuskar kundin dokokin Najeriya a watan Yulin da ya gabata.