Ta maka mijinta a kotu don rashin mazakunta
Wata matar aure mai suna Hasana Adamu ta maka mijinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta garin Nasarawan Siyi da ke karamar Hukumar Ganjuwa, Jihar Bauchi, inda take rokon kotun da ta raba aurensu da mijinta, domin ba shi da lafiyar mazakunta.Matar ta bayyana wa kotu cewa mijin nata mai suna Abubakar Lumo ya dauki […]
Wata matar aure mai suna Hasana Adamu ta maka mijinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta garin Nasarawan Siyi da ke karamar Hukumar Ganjuwa, Jihar Bauchi, inda take rokon kotun da ta raba aurensu da mijinta, domin ba shi da lafiyar mazakunta.
Matar ta bayyana wa kotu cewa mijin nata mai suna Abubakar Lumo ya dauki tsawon lokaci yana fama da rashin lafiyar mazakunta, don haka take rokon kotu da ta raba aurensu.
Ta ce mijin nata shekarunsa 60 a duniya, ita kuma shekaranta 27 kacal a duniya.
Da alkali ya tambayi mijin nata ko zai iya ba ta takarda sai ya bayyana cewa tabbas abin da ta fada gaskiya ne, ya dauki tsawon lokaci yana fama da rashin lafiyar mazakunta amma zai ci gaba da neman maganin gargajiya domin ba ta hakkokinta na aure.
Da take karin bayani, ta ce da ta san cewa ba shi da cikakkar lafiyar mazakunta, da ba ta aure shi ba, domin tana tsoron fada wa cikin masifa. Sai dai kuma mijin nata ya bayyana wa kotu cewa a gaskiya ba zai iya rabuwa da ita ba, domin ta iya kwalliya, ta iya girki sannan kuma duk lokacin da ya kalle ta yana samun natsuwa a zuciyarsa. Saboda haka ya roke ta da ta koma gidansa.
Hassana ta ce: “Kafin na gudu zuwa gidanmu, na shafe sama da watanni tara ba ya ba ni hakkokina na aure. Kawo cefane ba shi ne kadai hakkokin aure ba, don haka zai yi wahala in koma gidan mijina.”
Alkali Abdulkadir Usman ya dage sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan nan domin yin nazari da yanke hukunci.