Ta maka mijinta a kotu saboda ba ya Sallah
Wata matar aure mai suna A’isha Muhammad ta maka mijinta mai suna Sale Abdullahi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Tashar Babiye, tana rokon kotu da ta raba aurensu domin mijin nata ba ya yin salloli biyar a kowace rana sannan kuma ba ya yin azumin farilla na watan Ramadan; don haka ba ta […]
Wata matar aure mai suna A’isha Muhammad ta maka mijinta mai suna Sale Abdullahi a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Tashar Babiye, tana rokon kotu da ta raba aurensu domin mijin nata ba ya yin salloli biyar a kowace rana sannan kuma ba ya yin azumin farilla na watan Ramadan; don haka ba ta kaunar ta ci gaba da zama da shi.
Ta bayyana wa kotu cewa shekara biyar ke nan da aurensu kuma ta shiga gidan mijinta tana da ilimi daidai bakin gwargwado amma sakamakon yadda ba ya kula da addini, iliminta ya lalace, abubuwa da dama da ta haddace sun zube saboda mijinta ba ya kula da addini.
Sai dai kuma mijin nata ya gabatar da shaidu uku a gaban kotu, inda kotu ta yi masu tambayoyi daya bayan daya, dukkansu sun bayyana wa kotu cewa abin da A’isha take fada ba gaskiya ba ne, domin suna Sallah a masallaci daya tare da Sale Abdullahi saboda haka a ce ba ya Sallah ba ya azumi ba gaskiya ba ne.
A’isha da mijin nata suna da zama ne a kauyen Kusi da ke yankin karamar Hukumar Bauchi kuma yanzu haka sun haifi ’ya’yansu biyu da mijin nata.
To, sai dai kuma da kotu ta tambayi A’isha shin za ta koma gidan mijin nata? Sai ta bayyana cewa tabbas za ta iya komawa amma sai ya dauki alkawari a gaban kotu cewa idan ta koma gidansa zai sanya ta a makarantar Islamiyya domin ta ci gaba da karatu.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ishak Magani ya dage sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan gobe domin yin nazari da yanke hukunci kuma ya bukaci mijin nata da ya je su tattauna da mahaifin A’isha kafin ranar su dawo kotu.