Ta maka mijinta a kotu saboda ya ki kai ta Saudiyya

Wata mata ta maka mijinta a kotun Musulunci saboda ya ki zuwa da ita kasar Saudiyya

Ta maka mijinta a kotu saboda ya ki kai ta Saudiyya

Wata kotun shari’ar Musulunci (Tsohuwar ajiya)

Wata mata ta maka mijinta a kotun Musulunci tana neman hakkinta saboda ya ki zuwa da ita kasar Saudiyya.

Matar, mai shekara 45 ta shaida wa kotun Musulunci da ke yankin Rigasa a Jihar Kaduna cewa shekarunsu hudu da aure, amma wata biyu kacal mijin nata ya ciyar da ita, ita ke fadi-tsahin ciyar da kanta.

Ta bayyana cewa, mijin nata “ya gaya min cewa an sallame shi daga aikinsa na direba, amma ya samu wani aiki a kasar Saudiyya, inda ya bukaci in yi hakuri ya kuma yi alkawarin cewa zai dauke ni mu tafi can tare.

“Tun daga lokacin ni nake ciyar da kaina; har rancen kudi na karbo masa don ya biya kudin tafiyar, amma da ya samu abin da yake nema, sai ya ce ya sake ni.”

Sai dai ta ce ba ta da wata shaida game da zargin kudi da ciyarwan da take mishi, Allah ne shaidanta.

Amma shi wanda ake zargin ya musanta, inda ya bayyana wa kotu cewa shi ya jima da sakin ta.

Daga nan ne alkalin kotun, Malam Anas Khalifa, ya tabbatar da rabuwar ma’auratan.

Amma ya ce kotun za ta saurari sauran tuhume-tuhumen da ake wa mijin ne kawai idan aka kawo shaidu.

(NAN)

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja