Ta matse masu can!

Allah  Ma ji rokon bayinsa ne, musamman ma wadanda aka cuta, domin kuwa addu’ar bayinSa tamkar danko take, ba ta faduwa kasa banza. Muddin dai bayin Allah za su yi hakuri, su yi imani da kudurar Mahaliccinsu, to za su ga sakayyar ayyukan da ake yi don a cutar da su. Irin haka ne ya […]

Ta matse masu can!
Ta matse masu can!

Allah  Ma ji rokon bayinsa ne, musamman ma wadanda aka cuta, domin kuwa addu’ar bayinSa tamkar danko take, ba ta faduwa kasa banza. Muddin dai bayin Allah za su yi hakuri, su yi imani da kudurar Mahaliccinsu, to za su ga sakayyar ayyukan da ake yi don a cutar da su. Irin haka ne ya faru a makon jiya sa’ilin da wuya ta yi wuya, tsanani ya yi tsanani, sai kawai ga sauki nan Allah Ya saukar wa bayinSa, domin kuwa sun fara ganin alamun mafita daga ja’ibar da ta jefa su cikin kangin shugabanni marasa imani.
Kodayake kawunan manyan shugabannin da ke cutarwa maimakon mulki, wadanda suka daura bakar gaba da talakawa sun fara farrakuwa tun sa’ilin da  rashin  adalcinsu ya wuce kan talakawa, ya fara komawa kansu, amma ba a gansu a rana ba suna jifan  juna` da miyagun jafa’i kamar na wannan karon. Rannan kwatsam sai ga tsohon  shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya nannado wasu babbakun maganganu cikin wata wasika, irin ta cin mutunci da tijara, ya aike wa dan gidansa, kuma dan lelensa, Dokta Goodluck Ebele Jonathan.
Bisa ga dukkan alamu Cif Obasanjo ya takali Goodluck ne da fada, shi ya sa ya fara goranta masa, domin  an ce a ranar fada ne ake gori. Hakan kuma ya sa Jonathan ya fusata, amma har yanzu bai mayar da martani ba, yana jira ne ya shanye takaicin abin da wasikar da  Obasanjo ta kunsa, sa’annan shi kuma zai nuna masa cewa ruwa ba sa’an kwando ba ne, domin zai tayar da gagarumar gobara a gidan Obasanjo wanda ya san ba zai iya fitowa ya kashe ba, domin yana da walkin bunu a kugunsa.
Ba shakka  Obasanjo na sane da  cewa baki ya san abin da zai fada, amma bai san amsar da za a mayar masa ba. Idan kuwa haka ne, to me zai kai shi  kirari, sa’annan ya kirbawa cikinsa wuka? Ai shi da Shugaba Jonathan tamkar Tukura da Bako ne, dukkansu Umbutawa ne, ‘ya’yan jam’iyyar da ke wahalar da talakawa ce. Akwai wani bambanci ne tsakanin zarge-zargen da Obasanjo ya yi wa Jonathan da kuma irin ta’asar da aka tabbatar  ya sha tafkawa a lokacin da yake rugurguza kasar nan, da kuma daukaka matsayin ‘yan kabilarsa?  To wadanne hujjojin Obasanjo na yin rashin mutunci irin haka ga mutumin da ya tattago daga kauyensu, ya kuma cicciba shi bisa babban mukami? Tsananin batan basira ce ta janyo haka, ko kuwa kidahumanci da neman tayar da zaune tsaye ne da rana tsaka gagal? To wanda duk ya rubuta takarda ga ko wanene kuwa zai jira amsa, kuma tabbaci hakika  mai son da Jonathan zai yi zai zame kayan kwalbar da Obasanjo zai baras, daga bisani kuma ya taka, ya yanyanke kafafu.
A matsayin Cif Obasanjo na babban dan koren Amurka a kasar nan ba wannan ne karon farko da ya ke cin mutuncin shugabannin kasar nan irin haka ba. Ya taba yin amai, ya lashe, sa’ilin da ya mika mulkin farar hula ga Alhaji Shehu Shagari, daga bisani ya nemi ya karasa gurgu da tadiye, domin kuwa ba irin dattin  da bai debo ya zuba mar ba, don ya bakanta shi, bai kuma huta ba sai da ya ga bayansa. Sojoji ‘yan uwansa ma da suka mulki kasar nan ba su tsira daga kaidinsa ba, jikin Janar Babangida cike yake da tabban sharrinsa, da su kuma za shi kiyama. Haka nan ma ya sanya janar Sani Abacha a gaba, amma da yake Obasanjo bai daddara ba da cin kasa ba sai ga shi nan ya ci ta suri. Dangane da haka ne Janar Abacha ya tarkato shi, ya jefa shi a gidan jarun, ya  ce ya je ya mace a can.
Ko da yake Obasanjo ya sha yin tasiri a makirce-makircensa, amma an tabbatar da cewa  Amurkan da ke ingiza shi ce ke taimaka masa yana yin nasara, yanzu kuma ba wanda zai debe zato cewa ya yi haka ne ba don amfanin ‘yan Najeriya ba, sai don a janyo hankulan kasashen Yammacin Turai da Amurka game da illolin Gwamnatin Jonathan da niyyar muzanta shi har su canja ra’ayinsu game da shi nan gaba. Wannan abin dai na da alaka da zaben 2015, kuma tun da askin da ake yi wa Jonathan, don ya ji dadin yakin neman zabe, ya fara gusowa gaban goshi, tilas ne ya yi ta mutsu-mutsu, daga karshe kuma askar wanzam ta yi gardama, ta zabge mar  rabin naman kai, har ma da na kumatu.
Ko da yake ba domin talakawan Najeriya ne Obasanjo ya yi wannan tonon silili game da miyagun dabi’u da halayen Jonathan ba, don sun fi kowa kwana sanin haka, amma talakawa cewa suke ai gara da aka yi yunwa, ga shi nan halin kowa na fitowa fili, kuma sakamakon haka watakila za a samu sa’ida. Fatar da talkawa ke yi shi ne Allah Ya tabbatar da alherin da ke tatare da wasikar Obasanjo, idan kuma sharri ne Ya mayar bisa kansa. Tsakanin Obsanjo da Jonathan ba mai yiwa wani fatan alheri, kowa na neman kwashe kafafun danuwansa ne, to sai a ce ta matse masu can.