Ta mayar da gurgun kare dan riko

Mai gabatar da shirin talabijin da rediyo, Angel Wong chui Ling, ta ce ta yanke daukar kwikuyo dan shekara biyu a matsayin dan riko. “Yana bnukatar gida da damar walwala ta rayuwar dabba abar so ga iyali, ni kuwa zan iya samar masa da wadannan abubuwa,” inji Wong.Ta ce ta dauki rainon kwikuyo Patrick, wanda […]

Ta mayar da gurgun kare dan riko

Wong, wadda ta dauki kare dan rikoMai gabatar da shirin talabijin da rediyo, Angel Wong chui Ling, ta ce ta yanke daukar kwikuyo dan shekara biyu a matsayin dan riko. “Yana bnukatar gida da damar walwala ta rayuwar dabba abar so ga iyali, ni kuwa zan iya samar masa da wadannan abubuwa,” inji Wong.
Ta ce ta dauki rainon kwikuyo Patrick, wanda ke da hadaddun kafafuwa, daga hannun masu fafutikar kyautata rayuwar karnuka na kasar Malesiya, kimanin wata biyu da suka shige.
Ta ce tana yi masa wanka, ta ciyar da shi, sannan ta hada shi da dayan karenta, su biyu su kewaya, su yi tattaki, duk da yawan ayyukan da ke gabanta.
“Ina tashi da karfe hudu da rabi na safe don gudanar da shirin rediyo na barka da safiya, ama duk da haka ina kula da karnuka biyu,” a cewar Wong, wadda dayan karenta, nau’in Fei Mui ne.
A cewar, abin farin ciki ne mutum ya mallaki karnuka, don haka ta shawarci iyalai da su yanke shawarar daukar karnukan da ba su da gidajen kwana a matsayin ’ya’yan riko.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan