Ta mika jaririnta ga gidan marayu saboda haihuwarsa babu ido
Mahaifiyar wani jariri da ta haife shi babu idanu ta mika shi ga gidan marayu bisa hujjar cewa ba za ta iya ci gaba da rayuwa da jaririn ba. Jaririn mai suna Aledander K da ake wa lakabi da Sasha, mahaifiyarsa ta yanke hukunci mika shi ga gidan marayun ne a kasar Rasha don ya […]
Mahaifiyar wani jariri da ta haife shi babu idanu ta mika shi ga gidan marayu bisa hujjar cewa ba za ta iya ci gaba da rayuwa da jaririn ba.
Jaririn mai suna Aledander K da ake wa lakabi da Sasha, mahaifiyarsa ta yanke hukunci mika shi ga gidan marayun ne a kasar Rasha don ya samu wadansu iyayen da za su iya ci gaba da rayuwa da shi. An haifi jaririn ne a watan Afrilun bana.
Likitocin a birnin Siberian a yankin Tomsk sun tabbatar da rashin idanun Sasha, jaririn yana dauke da cutar ‘SOD2 anophthalmia’ ta rashin idanu, bayan wannan yana cikin koshin lafiya. Yanzu haka hukumomi suna ci gaba da lura da jaririn. Larurar da aka haifi Sasha aba ce da ba a cika samu ba, saboda wani lokaci ana iya haifar jarirai da larura daban-daban a jikinsu.
Wata likita da take lura da Sasha ta ce, “Wannan jaririn bai da bambanci da sauran yaran da ke da idanu saboda yana wasa yana murmushi kamar sauran jarirai, yana sha’awar yin wasa da kuma saurin yin fara’a.”
Idan ana son a kwatanta Sasha a cikin sauran jarirai ana iya yi masa da lakabi da mai yawan murmushi cikin nishadi, yana murmushin ne a duk lokacin da ya ji muryar da ya saba da ita. Mahaifiyar Sasha ta rattaba hannu a takardar asibitin da take kai shi gwaji kan kin ci gaba da kula da dan da ta haifa. Ba a bayyana labarin mahaifin Sasha ba, a wajen da za a rubuta sunan mahaifi an bar wajen haka babu suna. Mahaifiyar Sasha ta ce, a ci gaba da lura da Sasha har zuwa lokacin da zai samu wadansu iyayen. Saboda a yanzu haka akwai matakai masu tsauri a kasar wajen karbar irin wadannan yara.
Sasha, yana daya daga cikin jarirai uku da aka yi wa rajista a duniya wadanda aka haifa ba su da kwayar ido kuma ba za su iya gani ba kwata-kwata.
A cewar kafar labarai ta The Siberian Times, za a rika saka wa Sasha wata kwaya a inda idonsa yake duk wata shida saboda kada halitttarsa ta sake canjawa idan ya girma.
Likitan asibitin Tomsk mai suna Tatiana Rudnikobich, ya ce, “Ana duba lafiyar Sasha kamar yadda ake yi wa sauran jariran da suke asibitin. Bayan Sashan da aka yi wa rajista a duniya wanda aka haifa babu ido wanda ya zama na uku. Akwai wani jariri mai suna Archie Innes, da ya zama na biyu wanda aka haifa a kasar Scotland, mahaifiyarsa mai suna Fiona kuma jaririn mai suna Steben Gould, suna zaune a Sydney, na kasar Australia. An haifi Archie dauke da larura jin sauti sannan ga rashin idanu.