Ta nemi a mayar da majalisun tarayya daya maimakon biyu

A yayin da kiraye-kiraye akan sake fasalin kasar nan ke cigaba da yaduwa, kungiyar Cigaban Zazzau (ZEMDA) ýta nemi da Najeriya ta koma yin amfani da majalisar dokoki ta kasa kwaya daya maimakon biyu da ake da su yanzu. A cewarsu, yin hakan zai taimaka matuka wajen rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen […]

Ta nemi a mayar da majalisun tarayya daya maimakon biyu

A yayin da kiraye-kiraye akan sake fasalin kasar nan ke cigaba da yaduwa, kungiyar Cigaban Zazzau (ZEMDA) ýta nemi da Najeriya ta koma yin amfani da majalisar dokoki ta kasa kwaya daya maimakon biyu da ake da su yanzu.

A cewarsu, yin hakan zai taimaka matuka wajen rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen tafiyar da al’amuransu, musamman na albashinsu da alawus-alawus. ZEMDA ta kuma nemi da koma wa yin amfani da kwamishinonin jihohi 10 kacal sannan kuma ‘yan majalisun jihohi a rika zabensu ta hanyar la’akari da yawan al’ummarsu dake gundumominsu.

Sun kuma bayyana ra’ayinsu ne a cikin wata kasida mai dauke da sa hannun shugabansu Malam Ahmad Maccido da kuma Sakatarensu Alhaji Muhammad Sani ýUwais suka kuma kai ofishin buga jaridar Aminiya dake Kaduna.

A cewarsu, akwai bukatar ‘yan Najariya su sake fasalin tunaninsu da zuciyarsu cikin gaggawa “Domin abubuwa ba za su cigaba da zama yadda aka saba ba watau wajen cin hanci da rashawa da rashin tarbiyya da kwadayi da kuma sauran munanan halaye. Saboda karuwar kafafen sada zumunta a duniyar yau, rayuwar ‘yan Najeriya na cikin hadari da rashin tsaro.

“Dole ne shugabanni da wadanda ake shugabanta su kasance masu bin doka ýda oda da kuma kare yancin dan Adam in ba haka ba kuwa babu wani irin sake fasalin kasar nan da zai taimaki rayuwar talakawan kasar nan,” in ji su. 

ýMajalisar ta kuma ce akwai bukatar magance matsalar tsadar tafiyar da gwamnati a kasar nan. Sun kuma koka da irin makudan kudaden da ake kashewa wajen biyan alawus da albashin ‘yan majalisun tarayya da na bangaren sashen zartaswa da kuma na shari’a ýda cewa ya yi yawa, wanda hakan ke shafar tattalin arzikin kasar nan.

“ZEMDA na bada shawarar cewa idan har ana son rage yawan kudade da ake kashewa wajen tafiyar da gwamnati musamman majalisu akwai bukatar a koma majalisa daya kawai a maimakon biyu da ake da su watau Dattawa da wakilai. Sabuwar majalisar zai samu wakilanta ne dai-dai da yawan al’ummar da suke wakilta a jihohinsu kuma za su yi aiki ne na wuncin gadi a biya su.

“Kuma kada a samu ministoci sama da 36 a gwamnatin tarayya. Sannan ko wace jiha kada ya nada kwamishinoni sama da 10. “’Yan majalisun jiha kuma wakilansu kada su wuce mutane dubu 200. Su ma ‘yan majalisun su kasance na wuncin gadi, ma’ana za a biya su ne kawai daidai da yawan zama da suka yi a majalisa,” in ji su.