Ta nemi kashe mijinta don ya kara aure
An gurfanar da wata mata da ta yi yunkurin halaka mijinta a gaban babban kotun shari’ar musulunci da ke birnin Zariya saboda ya kara aure.Matar mai suna Amina Muhammadu, wadda aka fi sani da Anti Fara, ‘yar shekara talatin da daya da haihuwa, ta yi yunkurin kashe mijinta mai suna Ibrahim Ali ne, wanda aka […]

An gurfanar da wata mata da ta yi yunkurin halaka mijinta a gaban babban kotun shari’ar musulunci da ke birnin Zariya saboda ya kara aure.
Matar mai suna Amina Muhammadu, wadda aka fi sani da Anti Fara, ‘yar shekara talatin da daya da haihuwa, ta yi yunkurin kashe mijinta mai suna Ibrahim Ali ne, wanda aka fi sani da Baba da ke zaune a gida mai lamba 180 kofar doka cikin birnin Zariya saboda auren da ya yi.
Mai gabatar da kara Kofur Abdul Lawal ya ce ana tuhumar Amina ce da yunkurin halaka mijinta ta hanyar kama masa mazakuta ta matse, inda ta fasa masa ‘yan marainansa da kuma yin barazanar kashe shi tare da amaryarsa.
Mai gabatar da kara ya ce wannan ne ya sanya aka kai ta ofishin ’yan sanda da ke kofar fada cikin birnin Zariya a ranar Alhamis 4/09/2014 da misalin karfe tara da rabi na dare.
Bayan kammala bincike ne aka gabatar da Amina Muhammadu a gaban Alkali domin fuskantar shari’a domin yin haka babban laifi ne.
Bayan mai gabatar da kara ya bayyana tuhumar da ake yi wa Amina (Anti Fara), sai Alkalin kotun Mai shari’a Muhammadu Ibrahim Dikko ya juya wurin Amina ya ce kin ji abin da ake tuhumar ki da aikatawa? har sau uku, Amina ta amsa, kuma ya kara tambayar Amina cewa ko kin aikata hakan? har sau uku, Amina ta amsa da cewa ta aikata.
Daga nan Mai shari’a Ibrahim Dikko ya ce Amina a matsayinta na matar aure ta aikata laifi babba a karkashin sashi na 215 da 233 da kuma 116 na dokokin shari’a.
Sai dai kuma Alkali Ibrahim Dikko ya amince da bukatar da mai gabatar da kara ya gabatar na neman a ba ma’auratan dama don su je su sulhunta tsakaninsu a gida, idan hakan bai yiwu ba sai su komo kotun a ranar 29 ga watan Satumbar nan don cigaba da sauraran karar.
Ita dai Amina ta yi kokarin hallaka mijinta ne a ranar da zai shiga dakin amaryarsa da misalin karfe tara na dare, inda ta gayyaci mijinta Ali baban A’i zuwa cikin dakinta ta ce tana da magana da shi, yana shiga sai ta kama mazakutarsa tare da ‘yan marainansa ta matse har sai da suka fashe, nan take Baban A’i ya fadi a sume bai farfado ba sai a gadon asibiti, St. Lukes da ke Wusasa Zariya.
Da Aminiya ta tuntubi Ango Ali Baban A’i domin jin ko yana da sha’awar cigaba da zama da matarsa Anti Fara, kasancewar suna kaunar junansu, kuma ga ‘ya’ya tsakaninsu, tun da ga shi Alkali ya ba su dama su yi sulhu a tsakaninsu? sai ya ce, sam shi ya gama zaman aure da ita, abin da ya sa ya nemi su je su yi sulhu shi ne, saboda ba ya bukatar su yi shari’a da ita albarkacin yaran da Allah Ya ba su. Ya ce ya bar ta da halinta Allah Ya raka taki gona.