Ta raba wa jama’a kyauta abinci don murnar karbar mulkin Buhari
Wata mai sayar da abinci a tashar mota ta NARTO da ke garin Katsina ta share wuni biyu tana bayar da abinci kyauta ga jama’a domin nuna farin karbar ragamar mulki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari za yi a yau. Matar mai suna Hajiya Hurera Ibrahim wadda ita […]
Wata mai sayar da abinci a tashar mota ta NARTO da ke garin Katsina ta share wuni biyu tana bayar da abinci kyauta ga jama’a domin nuna farin karbar ragamar mulki da Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari za yi a yau.
Matar mai suna Hajiya Hurera Ibrahim wadda ita ce Shugabar kungiyar Mata Masu Sayar da Abinci ta Katsina ta ce, ta yanke shawarar bayar da abincin da take sayarwa kyauta da sadaka ne domin murnar tare da yi wa wadannan bayin Allah addu’ar Allah Ya ba su ikon yin adalci, kuma Ya kare su da sauran shugabannin da aka zaba.
“Zuciyata ta ba ni cewa, wannan sabuwar gwamnati na da niyyar ciyar da talakawanta gaba ta hanyar habaka noma a Arewa, don haka yana da kyau mu yi ta yi musu addu’a tare da bayar da tamu gudunmawar,” inji ta.
Shugabatar ta ce, duk wanda ta ba abincin tana rokonsa ya yi addu’ar Allah Ya taimaka wa sababbin shugabannin su sauke nauyin da ya rataya a kansu.
Hajiya Hurera ta yi kira ga sauran ’yan kasuwa musamman na kayan abinci da sutura su taimaka wa mabukata ba tare da tsoron jari zai ragu ba.
Kusan duk wadanda suka samu abinci a wurinta da Aminiya ta ji ta bakinsu, sun yaba wa yunkurin da ta yi, inda suka cewa, Hajiya Hurera ta yi wani hannunka mai sanda ga jama’a kan su taimaka wa juna, maimakon zura wa gwamnatin da ta karbi mulki ido ta magance dimbin matsalolin kasar nan ba.
Nau’o’in abincin da Hajiya Hurera ta rarraba sun hada da tuwo da waina da shinkafa da nama da sauransu.