Ta rabu da mijinta don ya yi mata kashi a daki

Wata mata mai suna Rukayya Idris ta yi karar mijinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Uku da ke birnin Kano inda ta nemi kotun ta kashe aurenta da mijin a kan yi mata kashi a tsakar daki da yake yi. Rukayya Idris ta shaida wa kotun cewa tsawon wata shida da aurensu, idan dare […]

Ta rabu da mijinta don ya yi mata kashi a daki
Ta rabu da mijinta don ya yi mata kashi a daki

Wata mata mai suna Rukayya Idris ta yi karar mijinta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Uku da ke birnin Kano inda ta nemi kotun ta kashe aurenta da mijin a kan yi mata kashi a tsakar daki da yake yi.

Rukayya Idris ta shaida wa kotun cewa tsawon wata shida da aurensu, idan dare ya yi sai mijin nata ya tashi ya yi mata kashi a cikin daki, lamarin da ta bayyana da cewa yana cutar da ita.
Lokacin da kotun ta waiwaye shi game da da’awar matarsa wanda ake karar mai suna Hassan Idris ya amsa laifinsa inda ya ce sau daya tak ya taba yi mata kashi a dakin har kuma shi da kansa ya kwashe abinsa.
Har ila yau wanda ake karar ya nemi kotun da ta sulhunta tsakaninsa da matarsa kasancewar lalaura ce ta sa shi yi mata kashi a daki, kuma a cewarsa har yanzu yana kaunar ci gaba da zama da ita. Sai dai a nata bangaren Rukayya ta kafe cewa sai kotun ta raba auren nasu.
Alkalin Kotun Mai shari’a Ibrahim Sani Sarki Yola ya kashe auren a bisa hukuncin khul’i inda ya umarci matar da ta biya mijin Naira dubu 20 a matsayin kudin da ya kashe a lokacin aurenta.