Ta rasa aikinta kan kalaman nuna-wariya ga ’yan Najeriya
Kamfanin sufurin jiragen sama na British Airways ya kori ma’aikaciyarsa da ke aikin kula da fasinjoji saboda zargin yin kalaman kiyayya ga fasinjojin Najeriya da suka shiga jirgin daga birnin Landan zuwa Abuja. Manajan Kasuwanci na Yankin Afirka ta Yamma na Kamfanin, Kola Olayinka ya ce tuni suka kori ma’aikaciyar bayan da kamfanin ya kammala […]

Kamfanin sufurin jiragen sama na British Airways ya kori ma’aikaciyarsa da ke aikin kula da fasinjoji saboda zargin yin kalaman kiyayya ga fasinjojin Najeriya da suka shiga jirgin daga birnin Landan zuwa Abuja.
Manajan Kasuwanci na Yankin Afirka ta Yamma na Kamfanin, Kola Olayinka ya ce tuni suka kori ma’aikaciyar bayan da kamfanin ya kammala bincike kan batun.
Kamfanin ya kaddamar da bincike gadan-gadan biyo bayan bayyanar wani faifan bidiyo wanda ake zargin ma’aikaciyar da kanta ta dauki bidiyon inda ta rika yin kalaman nuna-wariya ga fasinjoji ’yan Najeriya.