Ta roki gwamnati ta inganta wutar lantarki a masana’antarta

kungiyar masu sana’ar kanikanci da ke kwakwacin Dawanau ta yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa ta roki gwamnatin Jihar Kano ta samar da wadatacciyar wutar lantarki a masana’antarta. Mataimakin shugaban kungiyar Malam Muhammad Umar Fagge ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Litinin.Ya ce idan aka wadata masana’antarsu da wutar […]

Ta roki gwamnati ta inganta wutar lantarki a masana’antarta
Ta roki gwamnati ta inganta wutar lantarki a masana’antarta

kungiyar masu sana’ar kanikanci da ke kwakwacin Dawanau ta yankin karamar Hukumar Dawakin Tofa ta roki gwamnatin Jihar Kano ta samar da wadatacciyar wutar lantarki a masana’antarta.

Mataimakin shugaban kungiyar Malam Muhammad Umar Fagge ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a ranar Litinin.
Ya ce idan aka wadata masana’antarsu da wutar lantarki, to za a kara samar da hanyoyin dogaro da kai a yankinsu, musamman ganin cewa akwai mutane fiye da miliyan biyu wadanda suke gudanar da harkokin neman abincinsu a nan.
Ya bayyana ana iya gyara kowace irin mota a masana’antarsu, ko a sabunta komai tsufar da ta yi, saboda kwararrun kanikawa da ake da su masu amana da aiki mai inganci,
Ya yi korafin suna fama da matsalar rashin wadatacciyar wutar lantarki a wannan masana’anta domin gudanar da aikace-aikacensu cikin sauki.
“Saboda girman masana’antarmu, mun kasa shi kashi hudu tare da yi masa shugabanni a kowace shiyya, ta yadda za su ji dadin gudanar da jagoranci bisa adalci, ina fata gwamnatin Jihar Kano za ta hada gwiwa da karamar Hukumar Dawakin Tofa domin kara inganta wannan wuri, musamman samar da karin na’urar raba wuta (transformer) akalla hudu.” Inji shi.
Sakataren tsare-tsare na kungiyar kanikawa reshen Jihar Kano Alhaji Murtala Audi ya sanar da cewa yanzu haka suna wani yunkuri na fara bada horo mai inganci ga dimbin matasa, domin kara samar da ayyukan dogaro da kai a wannan masana’anta ta kanikancin mota.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu