Ta roki gwamnatin Kano ta cika alkawari wajen biyan mambobinta kudin kwangilarsu

kungiyar ’yan kwangila ta Jihar Kano ta bukaci gwamnatin Jihar Kano ta biya bashin kudaden da mambobinta suke binta tun shekaru masu yawa domin farfado da kamfanoninsu. Wannan bayani yana kunshe ne cikin jawabin shugaban rikon kungiyar ’yan kwangila ta Jihar, Alhaji Auduwa Mai Tangaran yayin taron da kungiyar ta gudanar ranar Asabar da ta […]

Ta roki gwamnatin Kano ta cika alkawari wajen biyan mambobinta kudin kwangilarsu
Ta roki gwamnatin Kano ta cika alkawari wajen biyan mambobinta kudin kwangilarsu

kungiyar ’yan kwangila ta Jihar Kano ta bukaci gwamnatin Jihar Kano ta biya bashin kudaden da mambobinta suke binta tun shekaru masu yawa domin farfado da kamfanoninsu.

Wannan bayani yana kunshe ne cikin jawabin shugaban rikon kungiyar ’yan kwangila ta Jihar, Alhaji Auduwa Mai Tangaran yayin taron da kungiyar ta gudanar ranar Asabar da ta gabata, domin tattauna al’amuran kungiya da kuma halin da mambobinta ke ciki a yau.
Ya ce babu shakka ’yan kwangila a Jihar Kano sun kasance cikin mawuyacin hali cikin shekaru masu yawa, tare da zama cikin yanayi na tausayawa bisa rashin biyan su kudaden da suke bin gwamnati, sai dai ya sanar da cewa a halin da ake ciki, Gwamna Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alwashin biyan su kudadensu cikin dan lokaci kankane.
Ya kuma bukaci ’yan kwangilar su kara hakuri domin a cewarsa, al’amarin biyan kudade a gwamnati sai an yi hakuri da nuna juriya, domin aiki ne mai matukar daukar hankali saboda batun tantancewa.
“Da yardar Allah za mu yi aiki cikin amana wajen ganin an warware komai tsakanin gwamnatin Jihar Kano da daukacin mambobinmu, ta yadda harkokin kamfanonin su zai ci gaba da motsawa kamar yadda suke a da.”
Ya bukaci dukkan ’yan kwangilar su tabbatar da cewa takardun kamfanoninsu suna nan, sannan su sabunta wadanda suka kare kafin su fara aikin bada katin shaidar zama dan kungiya nan gaba kadan.
Ya kuma jinjina wa Gwamna Kwankwaso bisa hangen nesan da ya yi na yunkurin biyan kudaden ’yan kwangilar Jihar Kano ke bin gwamnati tun shekaru masu yawa.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi