Ta sa abokin majinta ya kashe majinta domin ta aure shi
Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta gabatar da wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Yakbyen Nanbol, da ta fito daga karamar Hukumar Langtang ta Arewa da ke jihar Filato tana zarginta da sanya abokin mijinta, dan shekaru 25 mai suna Nanbol Samson ya kashe majinta domin ta aure shi.Da yake bayani kan yadda al’amarin […]

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta gabatar da wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Yakbyen Nanbol, da ta fito daga karamar Hukumar Langtang ta Arewa da ke jihar Filato tana zarginta da sanya abokin mijinta, dan shekaru 25 mai suna Nanbol Samson ya kashe majinta domin ta aure shi.
Da yake bayani kan yadda al’amarin ya faru, abokin mijin nata Nanbol Samson ya bayyana cewa ya fara soyayya da Yakbyen Nanbol ne bayan da mijinta ya tafi aikin leburanci a wani kamfani a garin Fatakwal.
Ya ce mahaifiyar mijin wannan mata tana kauyensu ne, don haka yana yawan zuwa kauyen domin ganin mahifiyar tasa. Ya ce sun hadu ne shekaru da suka gabata, don haka yana zuwa gidansu a kowane lokaci.
Yadda ta sanya a kashe mijin nata
Nanbol Samson ya bayyana cewa a watan yulin da ya gabata ne suka fara soyayya da wannan mata, a lokacin da mijin nata ya yi tafiya zuwa garin Fatakwal. Ya ce a lokacin matar ta ce tana sonsa kuma za ta aure shi amma idan ya yarda zai kashe mijin nata.
Ya ce ya yi kokarin ya shawo kanta kan kada a yi haka ta bar shi kawai, amma ta ki, ta ce in dai yana son ya aure ta to ya kashe mijin nata.
Ya ce, “saboda ta ce tana sona, ni ma ina sonta, don haka na yanke shawarar kashe shi da wukar da na sayo a kasuwa.”
Ya ce, “A lokacin da na aikata wannan aika-aika na tafi gidansu ne da daddare na shiga cikin dakinsu na yi masa barazana da wata bindiga kirar gida. Ni da abokina muka dauke shi a kan babur muka tafi da shi muka je muka kashe shi, inda na yi ta caka masa wuka har ya mutu.’’
Wanda ya raka Nanbol Samson wajen kashe mijin wannan mata mai suna Philemon, ya bayyana cewa babu shakka ya san abin da ke tafiya tsakanin Nanbol Samson da Yakbyen Nanbol, sai dai bai san cewa abokin nasa ya yi niyyar kashe mijin nata ba ne. Ya ce abokin nasa ya ce ya zo ya raka shi zuwa wani waje, amma bai san cewa zai je ne ya kashe wani ni ba. Ya ce abokin nasa ne ya yi ta caka wa mijin matar wuka har ya mutu shi kuma yana tsaye yana kallonsa.
Ta karyata zargin
Da take bayani kan wannan al’amari, Yakbyen Nanbol ta tabbatar da cewa tana soyayya da Nanbol Samson, amma ta bayyana cewa ba ta ce ya kashe mijin nata ba. Ta ce, “muna cikin barci a cikin daki sai wani mutum ya zo ya kama mijina da karfi ya fita da shi, ni kuma na samu na fita ta windo na fada cikin gidan makwabtanmu. Banga fuskar mutumin da ya shigo dakin namu ba saboda duhu, makwabcinmu ne ya yi bayanin cewa Nanbol Samson ne ya kashe mijin nawa. Bayan da aka kama shi ne ya ce ni ce na ce ya kashe mijina kafin in amince mu yi aure.’’
Ta bayyana takaicinta kan yadda mijin nata yake yawan tafiya zuwa garin na Fatakwal ya yi watanni biyar zuwa watanni shida kafin ya dawo gida. Ta ce a lokacin da mijin nata ya yi irin wannan tafiyar ne Nanbol Samson yake zuwa ya same ta.
’Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin
Da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan al’amari, kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Filato Mista Chris Olakpe ya bayyana cewa wannan mata mijinta yana yawan tafiya zuwa garin Fatakwal ne don gudanar da aikin leburanci, shi ne a lokacin da baya nan matar take kiran wani abokinsa. Daga nan suka yanke shawarar cewa idan suna son su cigaba da zama tare su kawar da mijin daga duniya. Don haka a lokacin da mijin ya dawo daga Fatakwal abokin nasa ya zo ya tafi da shi wani wuri ya kashe shi.
Kwamishinan ya yi bayanin cewa, wannan magana tana nan a gaban sashin binciken aikata manyan laifuffuka na rundunar ‘yan sanda suna cigaba da bincike,kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.